A Rana Mai Kamar Ta Yau 27 Ga Watan Nuwamba 2020 aka kashe babban masanin kimiyyar nukiliya na Iran, Mohsen Fakhrizadeh, kusa da Tehran.

 An kashe babban masanin kimiyyar nukiliya na Iran, Mohsen Fakhrizadeh, a kusa da Birnin Tehran



A Rana Mai Kamar Ta Yau 27 Ga Watan Nuwamba 2020 aka kashe babban masanin kimiyyar nukiliya na Iran, Mohsen Fakhrizadeh, kusa da Tehran.


A ranar 27 ga Nuwamba, 2020, an zargi gwamnatin Isra'ila ta ka*she Fakhrizadeh a wani harin kwantan bauna da aka kai a Absard ta hanyar amfani da bindiga mai sarrafa kanta. A cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin a watan Yuni 2021, tsohon shugaban Mossad Yossi Cohen ya ba da tabbacin cewar isra'ila ke da alhakinta na kisan.


Ga yawancin Iraniya ba su da masaniya game dashi har sai ranar Juma'a 27 Ga Watan Nuwamba 2020 Ranar da aka kashe shi. Masanin kimiyyar nukiliyar Iran Mohsen Fakhrizadeh sananne ne ga waɗanda ke bin shirin nukiliyar Iran.


Majiyoyin tsaro na ƙasashen yammaci sun ɗauke shi babban mai tasiri a aikin nukiliyar kasar Iran. 


Kafofin yaɗa labaran Iran ba su wani ɗauki Fakhrizadeh da muhimmanci ba, inda suka ɗauke shi kawai a matsayin masanin kimiya mai binciken "kayan gwajin na cutar korona" a lokacin. 


Mark Fitzpatrick, mai nazari a cibiyar nazari ta Landan da ke bibiyar shirin nukiliyar Iran sosai, ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa: "Shirin nukiliyar Iran ya fi ƙarfin ace ya dogara da mutum ɗaya"


Shugaban Iran ya zargi Isra'ila da kisan babban ƙwararre kan shirin nukiliyarta.


Fakhrizadeh ne mafi shahara a cikin masana kimiyyar nukiliya na Iran, wanda ya jagoranci shirin a ƙarƙashin ma'aikatar tsaro.


Mohsen Fakhrizadeh Mahabadi masanin kimiyyar nukiliyar Iran ne kuma masanin kimiyya. An dauke shi a matsayin shugaban shirin nukiliyar Iran.


An haife shi a birnin Qom a shekara ta 1958, Fakhrizadeh ya shiga cikin rundunar kare juyin juya halin Musulunci bayan juyin juya halin Iran a shekarar 1979. Ya halarci jami'ar Shahid Beheshti, sannan ya sami digiri na uku a jami'ar Isfahan. Tun daga shekarar 1991, ya kasance malamin kimiyyar lissafi a jami'ar Imam Hossein.

Post a Comment

0 Comments