Afirka ta Kudu ta Saka sojoji sama da 3000 domin dakile ayyukan hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba.

 Afirka ta Kudu ta Saka sojoji sama da 3000 domin dakile ayyukan hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba.



Kimanin jami’an soji 3,300 ne za su shiga aikin ‘karfafawa' domin dakile ayyukan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a fadin Afirka ta Kudu.


Kakakin shugaban kasar Vincent Magwenya ya sanar a ranar Alhamis cewa jami'an soji 3,300 za su yi hadin gwiwa da 'yan sanda a "karfafa ayyukan yaki da masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a dukkan yankunan".


Aikin zai ci gaba har zuwa Afrilu na shekarar 2024 a matsayin wani bangare na "Operation Prosper" na Shugaba Cyril Ramaphosa don kafa doka da oda, in ji shi.

®Mahadi umar 


Post a Comment

0 Comments