An Tsayar Da Ranar Ci Gaba Da Sauraron Shari’ar Dan China Da Ummita
Dan China dai ya ce ya kashe wa marigayiya Ummita sama da N60m a lokacin da suke sharbar romon soyayya.
An tsayar da ranar da za a ci gaba da sauraren karar dan kasar Chinan nan Mista Frank Geng Quarong da ake zargi da kashe budurwarsa Ummulkusum Sani wadda aka fi sani da Ummita a Jihar Kano.
Babbar kotun jihar karkashin jagorancin mai shari’a Aminu Ado Maaji ta sanya ranar 6 ga watan Disamba domin ci gaba da sauraren karar.
A bara ne aka soma gurfanar da Mista Geng a gaban kotun da ke zamanta a Miller Road, inda ake tuhumarsa da zargin da laifin kisan kai wanda ya saba wa sashe na 221 na dokar penal code.
Kakakin babbar kotunan Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya ce an dakatar da shari’ar ce na tsawon watanni takwas saboda alkalin da ke jibintar shari’ar na cikin kwamitin alkalan da ke jagorantar shari’ar kotun sauraron kararrakin zaben da aka gudana a bana.
Ana iya tuna cewa, Mista Frank Geng Quarong, wanda ya gurfana a gaban Babbar Kotun Jihar Kano kan zargin kisan masoyiyarsa, Ummukulsum Sani Buhari, ya tabbatar da kashe ta da wuka.
Yayin da ake tuhumar wanda ake zargin ya shaida wa lauyan masu kara, Barista Aisha Mahmud cewa ya zo Najeriya ne a shekarar 2019, kuma yana aiki da Kamfanin Tufafi na BBY inda yake karbar albashin Naira miliyan 1.5 duk wata.
Mista Quarong ya shaida wa kotun cewa ya kashe wa marigayiya Ummita sama da N60m a lokacin da suke sharbar romon soyayya.
0 Comments