Gaskiyar Abunda yake faruwa da kamfanin MTN

 Kamfanin sadarwa na MTN a Nijeriya ya fitar da sanarwa inda ya nesantar da kansa daga ce-ce-ku-cen da ake yi cewa ya yafe wa kwastamominsa bashin da suka ci.



Tun da farko jama’a da dama a shafukan sada zumunta sun ta mika godiya tare da san barka ga kamfanin bayan sun ta duba asusun ajiyarsu ba su ga alamun ana bin su bashi ba.


Hakan ya sa batun yafe bashin ya zama daya daga cikin abubuwan da aka rika tattaunawa a Nijeriya da safiyar Asabar a shafukan sada zumunta.


Sai dai a sanarwar da kamfanin na MTN ya fitar a shafukansa na sada zumunta, ya bayyana cewa ya samu tangardar network ne.

“Kamfanin MTN Nigeria na tabbatar da cewa ya samu tangarda wanda hakan ya jawo cikas ga bangaren duba asusun ajiya. Sakamakon hakan akwai yiwuwar kwastamomi su rika samun sako na kuskure kan cewa an yafe musu bashinsu.


"Ba haka lamarin yake ba, bashin zai dawo daidai yadda yake idan aka gyara matsalar,” in ji sanarwar kamfanin.


Kamfanin ya tabbatar da cewa injiniyoyinsa na iyakar kokarinsu domin gyara matsalar.

Post a Comment

0 Comments