Julius Melema, ɗaya dan gwagwarmayar ƴancin Afirka a Jam'iyar EFF dake Afirka ta Kudu, ya maida martani masu kaushi Akan Palestine a cikin zauran Majalisa.

 "Don me zaku harba abu mai fashewa Asibiti?, Ko da Shugaban Ham**s zai gudu Asibiti don naiman Mafaka, babu wani dalilin da zai sa ku sanya Bam a Asibiti.


Ko da Dakarun Ham**s zasu gudu zuwa sansanin ƴan gudun hijira, baku da wani dalili da zaku kai hare-hare sansanin ƴan gudun hijira. Waɗannan Mutanen suna son shafe (Falasdinu) ne daga doron ƙasa. 


Abinda suke sunansa kisan kiyashi, kuma Babban laifi ne a tsakanin ƙasa da ƙasa, ya zama dole hukumar hukumta masu laifi ta duniya ta kama Netan--yahu, meyasa kuka bada damar a kama Shugaba Putin na Rasha, wadda bai aikata rabin abinda Netan--yahu yayi a Gaza ba?.





-Inji Julius Melema, ɗaya daga cikin ƴan gwagwarmayar ƴancin Afirka a Jam'iyar EFF dake Afirka ta Kudu, lokacin da yake maida martani masu kaushi a cikin zauran Majalisar. 


Fassara; Muhd Bala Afuwa.

Post a Comment

0 Comments