Ko kunsan dalilan da zasusa kotun koli tayi fatali da ƙarar APC a jihar Kano ?



Dalilan da zasu sanya kotun koli tayi fatali da ƙarar APC a jihar Kano 


Bayan kammala babban zaɓen shekarar 2023, jam'iyyar APC a jihar Kano ta shigar da ƙara gaban kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamna, tana kalubalantar nasarar da Injiniya Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP ya samu, a zaɓen gwamna na ranar 18 ga watan Maris 2023, suna kafa hujja da cewar wai babu sunan Abba a rijistar jam'iyyar NNPP da aka turawa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, sannan kuma sun ce wai adadin ƙuri'un da aka soke ya kamata a bayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba (Inconclusive), wanda zamu iya cewa kwata-kwata basu fahimci sabuwar dokar INEC ta 2022 ba. 


A cikin shekarar nan, jam'iyyar APM ta shigar da jam'iyyar LP da Peter Obi ƙara a gaban kotu, kan cewar Peter Obi ya fita daga PDP a ƙasa da kwanaki 30 ya shiga LP ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa, saboda suna so kotu ta soke takararsa, wanda kotu tayi watsi da ƙarar harma ta ci su tarar N400,000, suka daukaka ƙara, anan ma kotu tace dole sai dan jam'iyya ne yake da hurumi akan wannan, dan jam'iyyar ma ba kowa ba, sai wanda ya shiga zaɓen fidda gwani (primary election), idan anyi masa rashin adalci sai ya garzaya kotu.


Bari na koma batun soke ƙuri'u, a ranar zaɓe mambobin jam'iyyar APC sun dinga tayar da tazoma a rumfunan zaɓe don kada zaɓe ya gudana lafiya, domin suna so ƙuri'un kada su kai adadin da za'a iya bayyana wanda yayi nasara, wanda zaisa dole a tafi inkwankwulusib, ashe basu fahimci cewa sabuwar dokar tayi gyara akan haka ba, an kama tsohon MD na water board, tsohon MD na Kano line, da wani shima tsohon Kansila a Getso dake Gwarzo, wato dai suna so su aikata abinda Nasiru Yusuf Gawuna, Murtala Sule Garo da Lamin Sani Kawaji suka aikata a 2019, a mazabar Gama dake ƙaramar hukumar Nasarawa, wanda ya janyo Inkwankwulusib, saboda sashi na 26 na dokokin INEC.


A dokar zaɓe da aka yiwa gyara a 2022, komai yawan ƙuri'un da aka soke sakamakon rikici, to babu jam'iyyar da zata amfana dasu, kowa zai samu ZERO,

Post a Comment

0 Comments