Kotu ta daure sojan Amurka na bogi a Kaduna

 Hukumar da ke Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Nijeriya Zagon Kasa, EFCC, ta ce kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin zaman gidan yari na shekara biyu kan samun shi da laifin yi wa rundunar sojin Amurka sojan-gona.



Mai Shari’a Darius Khobo na Babbar Kotun Kaduna ne ya yanke masa hukunci bayan wanda ake zargin ya amsa laifinsa guda daya da ake zarginsa da aikatawa


Bayan yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara biyu, Mai Shari’a Khobo ya ba shi zabin biyan tarar naira 150,000.Sannan alkalin ya bayar da umarnin kwace wayar Kassah wato Samusng Galaxy A02 wadda ya yi amfani da ita domin aikata laifin.Reshen hukumar EFCC na Kaduna ne ya shigar da Jesse Joshua Kassah kara a gaban kotu bayan an kama shi a yankin Karji na jihar kan zargin damfar


Hukumar ta ce Jesse na amfani da sunan wani sojan Amurka Devaun Smith Wayne domin damfarar jama’


Zamba cikin aminci da yaudara na daga cikin manyan abubuwan da hukumar ta EFCC ke yaki da su a Nijeriy


Ko a kwanakin baya sai da hukumar ta EFCC ta kama wani matashi wanda ake zargi da yi wa matar Sarkin Bichi zamba cikin aminci ta naira miliyan 20.

Post a Comment

0 Comments