Kungiyar Kwadago ta Nigeria Labour Congress (NLC) da takwararta ta Trade Union Congress of Nigeria (TUC) sun janye yajin aikin da suka kwashe kwana biyu suna yi a fadin kasar.

 


Kungiyoyin sun bayyana haka ne ranar Laraba da tsakar dare bayan wata ganawa da suka yi da Malam Nuhu Ribadu, mai bai wa shugaban Nijeriya shawara kan sha'anin tsaro.



NLC da TUC sun ce sun janye yajin aikin ne bayan Malam Nuhu Ribadu ya tabbatar musu cewa za a hukunta mutanen da aka kama bisa zargin cin zarafin shugaban NLC Mr Joe Ajaero.


NLC da TUC: Yajin aiki 'yan kwadago 'ya durkusar da tattalin arziki a Nijeriya'

Kungiyoyin Kwadago na NLC da TUC ne suka ayyana tafiya yajin aikin tun tsakar daren Talatar da ta wuce, sakamakon wata takaddama da ta kaure tsakaninsu da gwamnatin jihar Imo kan zargin cin zarafin Mr Ajaero da 'yan sandan jihar suka yi, mako biyu da suka wuce.


Yajin aikin ya durƙusar da ayyukan bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe da na tasoshin jiragen ruwa da jiragen ƙasa da fannin man fetur da ma dakatar da karatu a wasu makarantun gwamnati a wasu sassan ƙasar.

Post a Comment

0 Comments