Ministan tsaron Isra'ila ya yi ikirarin kwace iko da yammacin Birnin Gaza

 Sojojin Isra'ila suyi ikirarin kwace iko da yammacin Birnin Gaza, a cewar ministan tsaron kasar, yana mai sanar da soma "mataki na gaba" na kutsen da suke yi ta kasa.



A yayin da yake magana da sojojin Runduna ta 36 da ke kudancin Isra'ila, Yoav Gallant ya ce: "A awanni 24 da suka gabata, mun kwace iko da yammacin Birnin Gaza, kuma mun soma mataki na gaba na hare-haren da muke kaiwa ta kasa."


Ya kara da cewa: "Da zarar mun matsa kaimi a wannan yaki, hakan zai matsa lamba kan Hamas kuma za mu yi nasara wajen kawar da kayan yakinta da hedkwatarta da gine-ginen karkashin kasarta."


Hare-haren da Isra'ila ta kaddamar ta sama da ta kasa a Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba sun yi sanadin kashe Falasdinawa sama da 11,000, fiye da rabinsu mata da kanananMutum fiye da 7,000 da suka hada da wadanda aka kora daga gidajensu da marasa lafiya da jami'an kiwon lafiya a Asibitin Al Shifa suna "kokarin kauce wa mutuwa sakamakon rashin ruwa da abinci" saboda kawanyar da dakarun Isra'ila suka yi musu, kamar yadda ofishin watsa labarai na Gaza ya bayyana.


A wata sanarwa da ofishin ya wallafa a manhajar Telegram, ya jaddada irin mawuyacin halin da mutanen suke ciki, yana mai bayyana cewa "babu abinci da ruwa da madarar da za a bai wa jarirai a Asibitin Al Shifa


"Bakwaini da ke fama da rashin abinci za su iya rasuwa a asibitin saboda rashin wutar lantarki, abin da ya sa aka fitar da su daga kwalaben da suke ciki," in ji sanarwaShugaban bangaren siyasa na Hamas ya ce kungiyar da ke Zirin Gaza ta shirta tsaf domin gwabza yaki na tsawon lokaci da sojojin Isra'ila.


A wani jawabi da aka nada kuma ya gabatar ranar Alhamis, Ismail Haniyeh ya jinjina wa Falasdinawa da kuma yadda suka hada kai wajen “wargaza sojojin Isra'ila da rage musu karfi ta kowacce fuska.”


“Idan har makiya suna so a yi yaki mai tsawo, karfinmu ya fi na makiyanmu kuma bijirewarmu ba za ta gushe ba,” yana mai nuna cewa “mayakanmu suna fafatawa a yaki da makiyanmu Yahudawa kuma za mu yi nasara,” a cewar Haniyeh.


Ya bayyana irin “nasarorin da mambobinmu suka samu a Zirin Gaza,” yana mai karawa da cewa “gwarazanmu suna fitar da mu kunya a Gaza, suna jajircewa da kuma cin galaba a kan makiyanmu da lalata ababen hawansu.”


“Duniya za ta ga lokacin da Rundunar Al-Qassam da masu taya ta aiki za su murkushe mamayar da Isra'ila ke yi a Gaza, kamar yadda suka yi shekara 18 da suka gabata.”r.." yara.

Post a Comment

0 Comments