Na Saki Matana Uku a Rana Daya Kuma Bazan Sake Yin Aure Ba a Rayuwata - Inji Wani Magidanci Da Ya Talauce

 Na Saki Matana Uku a Rana Daya Kuma Bazan Sake Yin Aure Ba a Rayuwata - Inji Wani Magidanci Da Ya Talauce 



Wani magidanci mai shekara 55 rana guda a fusace ya saki matansa guda uku ya bayyana dalilin da ya sa ya dauki matakin kuma ya sha alwashin ba zai kara aure ba.


Dattijon da ke zaune a Uganda, wanda aka bayyana shi da Mutiacya, ya bayyana a wata hira da Afrimax English cewa ya taba yin arziki kuma yana kula da iyalinsa sosai har sai da ya rasa aikinsa kuma babu hanyar samun kudin shiga.


Shi da matansa uku suna da ’ya’ya bakwai kuma suna zaune lafiya domin ba su da wata matsala a baya.


 Amma da ya daina samun kudin shiga, ya ce matansa uku sun masa nauyi kuma ba sa son girmama shi. Ya bayyana yadda matan suka raina shi da nuna rashin mutunci. 


Saboda takaici da bacin rai, Mutiacya ya yanke shawarar korar dukkan matan uku a rana daya domin su yi rayuwar kadaitaka.


Yayin da matan suka tafi, sun tafi tare da ’ya’yansu bakwai, haka ya zaɓi ya yi yaje wajen wasa da yaran wasu kuma yana kashe musu kuɗi. 


Yaran Mutiacya sun girma kuma wasunsu suna zaune a kasashen waje yayin da wasu ke zaune a Uganda. Ya ce a wasu lokuta suna ziyarce shi kuma su koma wurarensu daban-daban.


Da aka tambaye shi ko zai kara aure, sai ya ce “bazan sake yi ba”, yana mai nuni da cewa ya gaji da matsalolin da ke tattare da aure.

Post a Comment

0 Comments