Nijar ta soma aiki da tashar sola mafi girma bayan Nijeriya ta hana ta wutar lantarki.
Nijar ta soma amfani da tashar samar da hasken lantarki ta sola mafi girma ranar Lahadi domin cike gibin lantarki da kasar ke fuskanta bayan Nijeriya ta hana ta wuta saboda juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yuli, kamar yadda Ministan Ma’aikatar Makamashi na kasar ya bayyana.
A wani jawabi da ya yi a gidan talabijin, Mahaman Moustapha Barke ya ce tuni kamfanin samar da hasken lantarki na Nijar Nigelec ya tabbatar da "samun inganci na hasken lantarki" a Yamai babban birnin kasar da kuma biranen Dosso da Tillaberi.
Kasar Nijar na da wadataccen haske rana Tashar ta sola tana da fayafayan sola fiye da 55,000 wadanda za su iya samar da megawat 30 na hasken lantarki.
Ranar 25 ga watan Agusta aka so kaddamar da tashar sai dai an samu jinkiri ne saboda wasu kwararrun ma’aikatan da ke kula da ita sun daina aiki bayan juyin mulkin da aka yi a kasar, in ji Bark
Ya kara da cewa sauran ma’aikatan da ba su tafi ba ne suka tabbatar da wannan shiri ya soma aik
Ofishin jakadancin Fasansa a Nijar ya yi gargadi cewa akwai yiwuwar "fuskantar hatsari" saboda “ba a kammala tashar kamar yadda aka tsara ba
An kashe kusan CFA biliyan 20 (kwatankwacin $33m) wajen gina tashar, kuma an karbi akasarin kudin ne daga cibiyoyin bayar da rance na Faransa da kuma tallafin Tarayyar Tura
Nijar na fama da yawan daukewar hasken lantarki bayan Nijeriya, wadda ita ce take ba ta yawancin lantarkin da take amfani da shi, ta hana ta a wani mataki na jerin takunkuman da kungiyar ECOWAS ta sanya wa kasar saboda juyin mulkin da sojoji suka yi ranar 26 ga watan Yuli.i..”i.e.
0 Comments