Rundunar ƴan sandan Kano da ke arewa maso yammacin Nijeriya ta sanar da matakai da za ta dauka a ranar da Kotun Daukaka Kara za ta yanke hukunci kan zaɓen gwamna na jihar.
A makon jiya ne Kotun Ɗaukaka Ƙarar da ke zamanta a Abuja ta kammala sauraron ƙarar da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP ya ɗaukaka, kan hukuncin da Kotun Ƙararrakin Zaɓen gwamnan jihar ta yanke a watan Satumba.
Duk da cewa rundunar ƴan sandan ba ta faɗi ranar da ake tsammanin sanar da hukuncin ba, amma a bisa lissafin da doka ta tanada, ba zai wuce 18 ga watan Nuwamban da muke ciki ba.
“Dangane da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano za ta yanke, kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Muhammad Usaini Gumel tare da sauran shugabannin hukumomin tsaro, sun tura isassun jami’ai da kayan aiki don gano wurare masu muhimmanci a jihar, don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi tare da daƙile duk wani yunƙuri na tayar da hargitsi ko rashin bin doka da oda,” in ji sanarwar ƴan sandan a ranar Litinin.
Sanarwar ta bai wa al’ummar jihar tabbacin samar da isasshen tsaro kafin da ranar da kuma bayan bayyana hukuncin, “su ma mazauna jihar Kano ana sa ran za su bayar da gudunmawarsu wajen kaucewa karya doka.”
Dangane da haka, rundunar ƴan sandan ta ba da shawarwari kamar haka:
i. Ba za a yarda da taron mutane a ko ina ba da kuma kowace irin manufa
ii. A guji shiga cikin manyan ayyuka da bayar da shawarar shirya zanga-zangar tashin hankali da yin zanga-zanga ko wasu tarukan murna da ka iya jawo martani daga wani ɓangaren.
iii. Ƴan siyasa su guji yin kalamai barkatai waɗanda ka iya haifar da tashin ko kuma ɓata shirye-shiryen samar da tsaro da taɓa fannin shari'a.
Kwamishina Gumel ya jaddada cewa rundunar ‘yan sanda tare da sauran jami’an tsaro a jihar ba za su ba da damar ɓata sha’anin tsaro ba ga duk wani mara gaskiya da ke kokarin kawo cikas, "don haka ake kira ga jama’a su cigaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin lumana."
A ƙarshe rundunar ƴan sandan ta bayar da wasu lambobin waya da adireshin shafukan sada zumunta da al’ummar jihar za su iya tuntuɓa don gabatar da ƙorafi
Lambobin da shafukan su ne: 08032419754, 08123821575, 09029292926
Facebook: Kano State Police Command;
Twitter: Kano State Police Command (@KanoPoliceNG)
Instagram: Kano State Police Command
Tiktok: Kano State Police Command.
0 Comments