Sanatocin Arewacin Nijeriya sun bukaci Tinubu ya mayar wa Nijar lantarki

 Sanatocin Arewacin Nijeriya sun bukaci Tinubu ya mayar wa Nijar lantarki.



Sanatoci daga Arewacin Nijeriya sun bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mayar da wutar lantarki Jamhuriyar Nijar mai makwabtaka.


Sanatocin sun bayyana haka ne a wata sanarwa da suka fitar bayan wata tattaunawa da suka yi a Abuja ranar Talata.


Bukatar sanatocin na zuwa ne watanni hudu bayan Nijeriya ta katse wa makwabciyarta Nijar wutar lantarki bayan juyi mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Mohamed Bzoum a watan Yuli.


Muna rokon shugaban kasa kuma babban kwamandan askarawan Nijeriya kuma shugaban kungiyar ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu da ya dubi halin jinkai ya mayar da wutar lantarki a Jamhuriyar Nijar,” in ji Sanata Abdul Ningi, shugaban Sanatocin, a yayin da yake karanto sanarwar bayan taron.

Sai dai sanatocin sun yi kira ga sojojin na Nijar su mayar da mulki a hannun farar-hula da kuma yin biyayya ga abin da shugabannin Afirka suke so daga gare su na sakin Shugaba Bazoum da iyalansa.


“Sanatocin Arewa suna Allah wadai da babbar murya kan katsalandan da sojoji suke yi wa dimokuradiyya a wasu kasashen Afirka. Wannan kungiyar tana Allah wadai da juyin mulki a Nijar da ke makwabtaka da Nijeriya.


“Muna kira ga sojojin da ke mulki a Nijar su saurari bukatun sauran kasashe ta hanyar sakin Shugaba Mohamed Bazoum da kuma iyalansa domin zabar kasar da yake so.”


Tuni Nijar ta soma nema wa kanta mafita ta bangaren wutar lantarki bayan katse mata wutar da Nijeriya ta yi.


Domin ko a cikin watan nan sai da kasar ta kaddamar da megawatts 30 na wutar lantarki.

Post a Comment

0 Comments