Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi yace lokachin surutu ya kare don haka yanzu lokacin daukar mataki ne

 Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ranar Asabar ya ce lokacin surutu ya kare don haka yanzu lokacin daukar mataki ne a kan rikicin Gaza a yayin da yake kan hanyar tafiya Sudiyya domin halartar taron Kasashen Larabawa da na Musulmai.


"Batun Gaza ba na yin surutu ba. Ya kamata a dauki mataki," in ji Raisi a filin jirgin saman Tehran kafi ya tashi zuwa birnin Riyadh na Saudiyya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.



Ya kara da cewa: "A yau, hadin kan kasashen Musulmai yana da matukar muhimmanci."

Post a Comment

0 Comments