'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga sama da hamsin a Taraba, yayinda Yan bindigan suka kashe mutum Sama da Sha biyu kafin isar Yan sandan

 'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga sama da hamsin a Taraba, yayinda Yan bindigan suka kashe mutum Sama da Sha biyu kafin isar Yan sandan.



'Yan sanda da hadin gwiwar wasu jami'an tsaron Nijeriya sun kashe 'yan bindiga sama da hamsin a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin kasar, in ji rundunar 'yan sandan kasar.


Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Bali ranar Talata, ko da yake rundunar 'yan sandan jihar ta bayyana haka ne ranar Alhamis da maraice, kamar yadda kakakinta Abdullahi Usman ya shaida wa gidan talbijin na Channels Television.


Ya kara da cewa jami'an tsaron sun kai samame ne bayan sun samu korafi daga mazauna yankin cewa 'yan bindigar sun addabe su, abin da ya sa jami'an tsaro suka yi musu kwanton-bauna inda suka kashe fiye da hamsin.


“Rundunar 'yan sandan Jihar Taraba ta samu bayanai cewa daruruwan 'yan bindiga da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun kai hari kauyen Tonti a yankin Maihula na karamar hukumar Bali.


'Yan bindigar sun kai hari ne da asuba yayin da mutane suke sallar asubahi, inda suka rika yin harbi kan mai-uwa-da-wabi,” a cewar Abdullahi Usman.

Post a Comment

0 Comments