Yayin da Isra’la ta kwashe kwana 39 tana luguden wuta a Gaza, an tilasta wa asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da ke arewacin yankin daina aiki

 A yayin da Isra’la ta kwashe kwana 39 tana luguden wuta a Gaza, an tilasta wa asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya da ke arewacin yankin daina aiki, ko dai saboda ruwan bama-bamai da ake yi musu ko kuma rashin fetur da magunguna, a cewar jami’ai.


Su ma asibotin da ke kudancin Gaza suna fuskantar wannan kalubale.


Kungiyar bayar da agaji ta Palestine Red Crescent Society ta ce janareto daya tilo da ke samar da lantarki a Asibitin Al Amal a Khan Younis da ke kudancin Gaza ya daina aiki ranar Litinin, abin da ke barazana ga majinyata — yawancinsu suna cikin mawuyacin hali — da dubban mutane da suke neman mafaka bayan an kore su daga gidajensu.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce Isra’ila ta kai hari 100 a cibiyoyin kiwon lafiya tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, lokacin da ta kaddamar da hare-hare a Gaza bayan Hamas ta kai mata harin ba-zata.



Daraktan asibitin Gaza mafi girma a ranar Talata ya ce mutum 179, daga ciki har da jarirai da marasa lafiya wadanda suka mutu a dakin kula da marasa lafiya an binne su a cikin kabari guda a harabar asibitin.


“An tilasta mana rufe su a kabari daya,” in ji daraktan Asibitin Al-Shifa Mohammad Abu Salmiyah inda ya ce akwai jarirai bakwai da marasa lafiya 29 wadanda ke dakin marasa lafiya masu tsananin bukatar kulawa na daga cikin wadanda aka binne.

Post a Comment

0 Comments