Amurka ta kai hari kan wuraren da ta ce sojojin da Iran ke mara wa baya a Iraki ne ke amfani da su

 Amurka ta kai hari kan wuraren da ta ce sojojin da Iran ke mara wa baya a Iraki ne ke amfani da su


Sojojin Amurka sun kai hare-hare a wasu wurare uku da sojojin da Iran ke mara wa baya ke amfani da su a Iraƙi, bayan wani harin da aka raunata ma'aikatan Amurka a safiyar yau, in ji Sakataren Tsaro, Lloyd Austin.


Austin a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce: Sojojin Amurka sun kai farmakin da suka dace kuma daidai gwargwado kan wasu wurare uku da Kataeb Hezbollah ke amfani da su da kuma kungiyoyin da ke da alaƙa da su a Iraƙi.


“Wadannan madaidaitan hare-haren martani ne ga jerin hare-haren da dakarun sa kai da Iran ke ɗaukar nauyin kai wa jami’an Amurka a Iraƙi da Syria, ciki har da harin Kataeb Hezbollah mai alaƙa da Iran da ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Iran a sansanin jiragen sama na Arbil da safiyar yau," ya faɗa.




Shugaban Isra'ila Isaac Herzog ya ziyarci sojojin da suka mamaye yankin da ke kusa da Gaza a ranar Litinin.

Herzog ya wallafa wani hoto a shafinsa na X wanda ke nuna shi yana rubuta "Mun amince da ku," a cikin harshen Ibrananci a kan harsasan bindigogi don nuna goyon baya ga kokarinsu.

"Ina so in gode muku, ba abu ne mai sauki ba ko kadan, kuma ba abin wasa ba ne cewa sama da watanni biyu mutane suna nan," ya shaida wa sojojin.

Ya kara da cewa dole ne sojoji su samu cikakken goyon baya yayin da suke kan gaba da kuma da zarar sun dawo daga bakin aiki.


Post a Comment

0 Comments