Amurka ta kai hari kan wuraren da ta ce sojojin da Iran ke mara wa baya a Iraki ne ke amfani da su
Sojojin Amurka sun kai hare-hare a wasu wurare uku da sojojin da Iran ke mara wa baya ke amfani da su a Iraƙi, bayan wani harin da aka raunata ma'aikatan Amurka a safiyar yau, in ji Sakataren Tsaro, Lloyd Austin.
Austin a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce: Sojojin Amurka sun kai farmakin da suka dace kuma daidai gwargwado kan wasu wurare uku da Kataeb Hezbollah ke amfani da su da kuma kungiyoyin da ke da alaƙa da su a Iraƙi.
“Wadannan madaidaitan hare-haren martani ne ga jerin hare-haren da dakarun sa kai da Iran ke ɗaukar nauyin kai wa jami’an Amurka a Iraƙi da Syria, ciki har da harin Kataeb Hezbollah mai alaƙa da Iran da ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Iran a sansanin jiragen sama na Arbil da safiyar yau," ya faɗa.
0 Comments