Amurka ta yi ikirarin harbo jirgin yaki mara matuki da makami mai linzami da 'yan Houthi suka harba

 Amurka ta yi ikirarin harbo jirgin yaki mara matuki da makami mai linzami da 'yan Houthi suka harba



Wani jirgin ruwan yaƙin Amurka ya harbo wani jirgin yaƙi mara matuƙi da makami mai linzami da 'yan tawayen Houthi na Yaman suka harba, in ji rundunar sojin Amurka.


A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta fitar ta ce, jirgin yaƙin USS Mason [DDG 87] ya harbo wani makami mai linzami guda ɗaya a Kudancin Tekun Maliya da Houthis suka harba.


CENTCOM ta ƙara da cewa, babu wata ɓarna da aka samu ko ɗaya daga cikin jiragen ruwa 18 da ke yankin, sannan babu wanda ya samu raunuka, inda ya ƙara da cewa shi ne karo na 22 na yunƙurin kai hari kan jiragen ruwa na ƙasa da ƙasa da Houthis suka yi tun tsakiyar watan Oktoba.

Post a Comment

0 Comments