Ministocin kasashen wajen Burkina Faso da Mali da Nijar ranar Juma’a sun bayar da shawarar kirkiro tarayyar kasashen uku a wani bangare na hada kan kasahen don su zama a dunkule wuri daya.
Dukkan kasashen uku na karkashin mulkin soji inda a Mali da Burkina sojoji suka kwace mulki a 2020 da 2022, sannan a Nijar sojoji suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yulin da ya gabata.
Tuni dama suka kirkiri wata kungiya mai suna Alliance of Sahel States da zummar karfafa tsaro da bunkasa tattalin arziki a tsakaninsu.
A wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar bayan kammala taron kwana biyu a Bamako babban birnin Mali, ministocin harkokin wajen kasashen uku sun bayyana cewa “akwai babbar dama ta zaman lafiya da kwanciyar hankali da karfafa diflomasiyya da bunkasa tattalin arziki idan aka yaukaka dangantaka da alaka ta siyasa”.
Ministocin... bisa burinmu na kasancewa tarayya da za ta hada Burkina, Mali da Nijar muna bayar da shawarar kirkiro tarayya ta shugabannin kasashen kungiyar Alliance of Sahel States,” in ji sanarwar.
Ministan Harkokin Wajen Mali Abdoulaye Diop ya ce za su mika shawarar ga shugabannin kasashen, wadanda za su gana a Bamako a wani lokaci da ba a fayyace ba.
Kazalika gwamnatocin sojin kasashen uku sun hada wata gamayya da za ta tunkari duk wani matsin lamba daga kasashen waje game da komawarsu kan turbar dimokuradiyya da kuma magance hare-haren masu ikirarin jihadi da ke addabar kasashen.
0 Comments