An kama 'yan kasar Faransa hudu a Burkina Faso kan zargin leken asiri


An kama 'yan kasar Faransa hudu a Burkina Faso kan zargin leken asiri.



Wani jami'in diflomasiyya ya bayyana cewa mutum hudun sun je gyaran kwamfuta ne a ofishin jakadancin Faransa da ke Burkina Faso.

An kama ‘yan kasar Faransa hudu a Burkina Faso kan zargin leken asiri, kamar yadda wasu majiyoyi na diflomasiyya a Yammacin Afirka suka bayyana a ranar Talata.


Wani jami’in diflomasiyyar Faransa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai cewa “Faransawa hudu wadanda ke da fasfo din diflmasiyya da biza, ‘yan sandan Burkina Faso sun kama su a Ouagadougou a ranar 1 ga watan Disamba”.


“Wadannan ma’aikatan sun je Burkina Faso domin gudanar da ayyuka na kwamfuta a ofishin jakadancin Faransa,” kamar yadda majiyar ta kara da cewa.


“Gwamnatin Faransa na ci gaba da bin kadin shari’a kan lamarin da ke faruwa, amma ta yi watsi da zarge-zargen da ake yi kan an tura ma’aikatan Burkina Faso saboda leken asiri baya ga gyaran kwamfuta,” in ji majiyar ta diflomasiyya.


Faransa na bukatar a sake su


Majiyar ta bayyana cewa Faransa na son “a mayar da su kasar ba tare da bata lokaci ba”. Wani jami’in diflomasiyya na Faransa ya ce ma’aikatan na Faransa “abokan aikinsu na Burkina Faso sun san su”.


Mujallar Jeune Afrique ce ta soma bayar da rahoto kan wannan lamari a ranar Talata kan cewa an kama ma’aikatan hudu a Ouagadougou kan zargin leken asiri.


“Ana yin duk abin da ya kamata domin a sake su,” kamar yadda majiyar ta diflomasiyya ta kara tabbatarwa.

Post a Comment

0 Comments