An shirya taron ƙara danƙon zumunci da haɗin kan yan asalin ƙaramar hukumar Kaita.

 An shirya taron ƙara danƙon zumunci da haɗin kan yan asalin ƙaramar hukumar Kaita.





An shirya taron sada zumunci da neman haɗin kan al'umma yan'asalin ƙaramar hukumar Kaita, watau Kaita Local Government connect.


Katsina Post ta samu cewa, manufar taron na musamman shine domin ƙara ɗankon zumunci tsakanin yan'asalin ƙaramar hukumar Kaita da suke zaune a ko'ina a faɗin ƙasar.


Mashahuran mutane daga ko'ina sun halarci taron wadanda suka haɗa da shugabannin siyasa, ɗalibai, shugabannin gargajiya, da jami'an gwamnati. 

 

Haka kuma an karrama wasu waɗanɗa suke bada gudummawar wajen cigaban ƙaramar hukumar ta ɓangaren samar ma matasa aiki, bada ilimi da sauran bangarori. 


Sannan a yayin taron an bude asusu wanda a'lumma da dama sun bada gudunmuwa musamman ta kudi da bada guraben sanaoin da kere-kere, ilimin fasaha, kwanfuta ga matasa yan'asalin ƙaramar hukumar. 


A yayin taron da ya gudana a makarantar sakandare ta GSS Kaita, an zayyana ayyukan da wadannan kungiyar za ta bama muhimmanci a sabuwar shekara me zuwa.


Daga cikin waɗanda suka halarci taron sun haɗa da: Maigirma Sarkin Sullubawan Katsina, Hakimin Kaita, sai kuma, Alhaji Sabitu Mohammed Jifatu (Chairman, Jifatu Nigeria Limited), Alhaji Abdulmumini Abubakar- Tafidan Kaita(Chairman AA Moda Gallery).

 

Sauran sun haɗa da Hon. Faisal Kaita, Kwamishinan ma'aikatar ƙasa da tsare-tsare, Alh. Lawal T. Bosa, Alh. Haruna Maiwada, Comrade Garba Ibrahim Dankama.


Sannan akwai, Alh. Almustapha Balarabe, Dr. Kabir Yandaki, Dr. Kamil Balarabe 

Da sauransu

Post a Comment

0 Comments