An yi garkuwa da mutane 23 a Abuja


A daren ranar Asabar ne wasu ƴan bindiga suka yi garkuwa da wasu mutane ashirin da uku a unguwar Dei-Dei da ke karkashin karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya, Abuja.
Daily Trust ta gano cewa an yi awongaba da mutanen ne daga gidajensu da ke cikin wani rukunin gidaje da masu haya suka mamaye, tsakanin karfe 8 zuwa 9 na dare.

Mai Unguwar Dei-Dei, Ibrahim Galadima yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin Daily Trust a daren jiya, ya ce jami’an tsaron da ke yankin sun ceto bakwai daga cikin wadanda aka sace, bayan sun bi sahun masu garkuwa da mutane cikin daji bayan kimanin sa’a guda.

“Ina jin dai masu garkuwa da mutanen da suka guda da wadanda su ka sace a rukuni uku, sun lura da cewa muna bin su a kan hanyarsu ta zuwa cikin daji, sai suka bar wadanda abin ya shafa su tafi,” in ji wani Galadima wanda ya bayyana cewa gidan da abin ya faru sabon wuri ne da ba a fi wata shida da tare wa ba.

Daily Trust ta ce ba ta samu yin magana da kakin ƴansanda na Abuja ba har zuwa lokacin hada rahoton.

Post a Comment

0 Comments