Ana zargin sojojin haya na Faransa da taya sojojin Isra'ila yaƙi a Gaza.

 YANZU YANZU: Ana zargin sojojin haya na Faransa da taya sojojin Isra'ila yaƙi a Gaza.



Sama da sojojin hayar Faransa 4,000 ne suka shiga yakin Isra'ila a Gaza


Wani dan majalisar dokokin Faransa ya buƙaci gwamnatin kasar da ta binciki ‘yan kasar sama da 4,000 da ke yaƙi tare da sojojin Isra’ila da suka mamaye kasar, kan laifukan yaƙi a yankunan Falasdinu.


Thomas Portes daga jam'iyyar La France Insoumise [LFI] ya rubuta a kan X cewa ya aika da wasiƙa ga Ministan Shari'a Eric Dupond-Moretti, yana neman a gudanar da bincike kan sojojin Faransa 4,185 da ke yaƙi tare da sojojin Isra'ila a Gaza.


Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci Isra’ila da kada ta “dakatar da Gaza” ko kuma ta kai hari ga farar hula ba gaira ba dalili.


Da yake jadada cewa ya kamata Faransa ta yi adalci wajen yi wa sojojin hukunci idan aka same su da aikata laifukan yaƙi, Portes ya ce zai daukaka ƙara zuwa ofishin mai gabatar da kara.


Portes ya ce ba za a amince da shigar 'yan kasar Faransa cikin laifukan ba, idan aka yi la'akari da laifukan yaki da sojojin Isra'ila ke aikatawa a Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan.


Wasu kungiyoyi da dama ne suka bayyana damuwar tun da farko, ciki har da kungiyar Faransa Palestine Solidarite [AFPS], wacce ta fitar da wata sanarwa da ta bukaci a dauki matakin hukunta ‘yan kasar Faransa da ke da hannu a laifukan yaki.

Post a Comment

0 Comments