Ƙasar Amurka ta fara damuwa da tsadar makamai masu linzami da take amfani

 ⚡️🇺🇸 AMURKA TA FARA KOKAWA 😢



Ƙasar Amurka ta fara damuwa da tsadar makamai masu linzami da take amfani da su a kan jiragen Ansarullah marasa matuƙi da take cilla su cikin Isra'ila, kasancewar ƙasar ana binta bashi na tiriliyoyin daloli.


 A cewar wani jami'in Sojin Amurka, Amurka tana yin amfani ne da makami mai linzami ƙirar SM-2 da tsadar shi ta kai dalar Amurka miliyan biyu da dubu ɗari ($2.1m) wajen daƙile jiragen marasa matuƙi da ƙasar Yemen ke harbawa wanda tsadar su dalar Amurka Dubu biyu ($2,000)


Zuwa Yanzu Amurka ta kama jiragen na Yemen har guda 38 jimlar kuɗin da suka kashe ya kai Dalar Amurka Miliyan Saba'in da tara da dubu ɗari takwas ($79.8m) yayin da su kuwa Husiyyun kwatakwata jiragen nasu kuɗin su Dalar Amurka dubu saba'in da shida ne ($76,000).

 

Sannan ga wannan sabuwar rundunar data kafa mai suna 

'Operation Guardians of Prosperity'

Wacce zata yi yaƙi da ƙasar Yemen ta ruwa wacce Allah kaɗai ya san iya asarori da Amurka zata yi saboda shirin da Ansarullah suka yi inda suka tabbatar da cewa Teku zata zama ƙabarin sojojin na Amurka don sun riga sun shirya suna da Makaman da ba'a ma san su ba waɗan da zasu tarwatsa duk wani jirgin ruwan yaƙi na Amurka daya kusanci Babul Mandeb a Tekun Bahar maliya.

Kar mu manta abu ɗaya fa kawai suka ce


Ba zasu bar duk wani jirgin ruwan Israila ya wuce ba matuƙar ba'a kaiwa Palasɗinawa Abinci da magani ba.

Wato banda kisa da Bomb har da yunwa da ciwo aka so kashe Palasɗinawa?


Allah ka yi jin ƙai ga wanda ya ƙirƙiro Ansarullah yake basu makamai da Atisayen soji har suka girma suke iya tsole idon Kafurawan Duniya.

Allah ka taimaki duk mai taimakon su.

Ka taɓar da duk maƙiyin su

Domin tsarkin zuciyar Annabi saww.


20/12/23

Shehu Al-ja'afaree Kaduna

Post a Comment

0 Comments