Babban Bankin Kasa CBN Zai Garƙame Dukkannin Asusun Bankin Da Ba a Haɗa Shi Da BVN Ba

 Babban Bankin Ƙasa (CBN) ya bada umarnin dakatar da dukkannin asusun bankin da ba a haɗa da shi da lambar tantance asusan bankuna (BVN) da Lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) ba daga cire kuɗaɗe, daga watan Afrilun 2024.



Tsarin mai suna “Post No Debit”, tsari ne da bankuna ke amfani da shi wajen ƙaƙabawa asusu takunkumi, ko dukkannin wani nau’i na fitar da kuɗi daga cikinsa.


Da zarar tsarin ya fara aiki kuma, babu wani mai amfani da bankunan da bai cika ƙa’idar BVN da NIN ɗin ba, da zai iya fitar da kuɗinsa.


Umarnin na CBN na ɗauke ne ta cikin wata sanarwa, da bankin ya fitar, tare da aikewa ɗaukacin bankunan ƙasar nan, a ranar Juma’a.


Sanarwar ta kuma ƙara da bayyana cewar, wajibi ne a sake tantance dukkannin BVN da NIN ɗin da aka haɗa da Asusun bankuna da Wallets, zuwa 31 ga watan Janairun 2024.


Sanarwar dai, na ɗauke da sa hannun, Daraktan Sashen Kula Da Tsarin Biyan Kuɗaɗe na Bankin, Chibuzo Efobi, da Daraktan Sashen Kula Da Tsare-Tsaren Kuɗaɗe, Haruna Mustapha.

Post a Comment

0 Comments