Bayanin gaskiya game da batun rufe bankunan Online da suka hada da; Opay, Palmpay, Moniepoint, Kuda, Wema da sauran su.
A makon da ya gabata babban bankin Najeriya ya bawa bankunan ajiyar kudi (DMBs) umurnin rufe duk wani asusun ajiyar kudi da ba shi da BVN da NIN daga farkon shekara mai zuwa.
Da yawan bankunan Online irin su Opay, Palmpay, da Kuda na ba mutane damar bude asusu ta hanyar amfani da lambar waya kawai, ba tare da sanya BVN ko NIN ba.
Sabanin bankuna na zahiri da sai kana da BVN da NIN, amma bankunan Online sun takaita shiga ko fitar kudi akan Naira dubu hamsin a asusu mai matakin tsaro na farko.
Sai dai CBN ya fitar da sanarwar da ke cewa: "Dole ne duk masu asusun ajiyar kudi da ke da matakin tsaro na farko ya makala BVN da NIN, kamar yadda yake dole masu mataki na biyu da uku su saka BVN da NIN, gaza hakan zai sa a rufe asusun."
Wannan sanarwa ta saka anata yada labari a kafofin sada zumunta cewa za'a rufe dukkannin Bankunan Online, duba da cewa suna bada damar ana bude asusu ba tare da an saka BVN ko NIN ba.
Wannan chakwakiyar ta shafi bankuna irin su Opay, Palmpay, Kuda da sauran bankunan Online masu yawan gaske, amma bata shafi bankunan Moniepoint da Wema Bank da sauran manyan bankunan zahiri ba.
A yanzu ya zama dole ga kowane bankin Online da ya bukaci BVN da NIN akan kowane asusun ajiyar da aka bude a cikin shi ko kuma a rufe shi.
Itama fadar shugaban kasa ta karyata labarin cewa, za'a rufe dukkannin Bankunan Online, sai dai tace kowane Banki dole yabi tsarin da Gwamnati ta kawo.
A yanzu haka cikin kwanakin nan, bankunan zahiri da dama sun daina nuna bankunan Online idan za'a tura kudi, wanda yake nuni da cewa suna kokarin katse alaka dasu.
Sannan akwai yiwuwar karawa Bankunan Online haraji, wanda hakan zaisa su fara cire Charges mai yawa ga masu ta'ammuli da bankunan.
✍️ Comr Abba Sani Pantami
0 Comments