Babban banki Najeriya CBN ya amince da kudin kirifto.


Babban banki Najeriya CBN ya amince da kudin kirifto.



A baya CBN ya hana bankunan kasuwanci na Nijeriya hada-hada da kudin na kirifto saboda rashin tsari da tabbas dinsa.

Kirifto ya samu karbuwa sosai musamman tsakanin matasa a Nijeriya./Hoto: Reuters

Babban Bankin Nijeriya, CBN, ya amince bankuna da daidaikun jama'a su rika mu'amalar kasuwanci da kudin intanet na kirifto.


A wata sanarwa da CBN ya fitar ranar Juma'a ya bukaci bankunan kasuwanci su yi watsi da matsayinsa na baya na haramta mu'amala da kudin na kirifto, kamar yadda kafafen watsa labarai na kasar suka rawaito.


Sanarwar ta ambato Daraktan Tsare-Tsare na Kudi da Dokokinsu na Bankin, Haruna Mustafa, yana cewa an dauki matakin ne sakamakon tagomashin da kudin kirifto yake samu a kasuwannin duniya.


Darajar kudin kirifto na Bitcoin ta zarta dala dubu 40

“A watan Fabrairun 2021, CBN ya fitar da sanarwar hana bankuna da sauran cibiyoyin kudi gudanar da asusai na kudin kirifto sakamakon hatsarinsa na taimakawa wurin halasta kudaden haramun da kuma daukar nauyin ta'addanci da kuma rashin dokoki," in ji sanarwar.


Sai dai ta kara da cewa yanzu Babban Bankin Nijeriya ya yi la'akari da yadda tsarin "duniya ya nuna bukatar sanya ido" kan harkokin kudin kirifto da kuma bayar da dama a yi amfani da shi.


CBN ya jaddada bukatar bin sabbin dokokin da hukumomin da ke sanya ido kan harkokin kudi suka fitar wajen amfani da kirifto.

Post a Comment

0 Comments