CIKAKKEN ABUNDA YA FARU SHEKARU 8 DA SUKA WUCE AKAN KISAN-KIYASHIN DA SOJOJI SUKA YI WA MUSULMI A ZARIYA.

CIKAKKEN ABUNDA YA FARU SHEKARU 8 DA SUKA WUCE AKAN KISAN-KIYASHIN DA SOJOJI SUKA YI WA MUSULMI A ZARIYA 
Daga Cibiyar Wallafa (www.cibiyarwallafa.org)

A ranar Alhamis, 28 ga Safar 1437H, daidai da 10/12/2015, bayan kammala zaman juyayin ranar wafatin Manzon Allah (S), Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayar da sanarwar taron saka tutar Mauludin Annabi (S), wanda ya ce za a gudanar da bikin a yammacin ranar Asabar 1 ga watan Rabi’ul Auwal, 1437 (12/2/2015).

A shekarun da suke gabanin nan, rundunar soja ta saba gabatar da bikin yaye sabbin kuratan sojojinta a Zariya a duk watan qarshen shekarar Miladiyya a ranar Juma’a da safe ne. Sai dai a wannan shekarar, ba zato ba tsammani sai suka maishe da bikin nasu ya koma Asabar 12 ga Disambar 2015, kuma da yammaci, maimako Juma’a da safe kamar yadda suka saba gabatarwa a tsawon shekaru. Wannan ya ba su damar ya zama rana da lokacin bikin nasu ya yi daidai da rana da lokacin taron sauya tutar Mauludi da Harkar Musulunci ta ayyana za ta gabatar a Husainiyyah Baqiyyatullah a wannan ranar.

Harkar Musulunci ba ta yi tunanin ta dage taronta a wannan ranar ba da ta riga ta ayyana ba, ganin cewa wuraren da za a gudanar da taruka biyun ba kusa suke da juna ba, don haka, babu wani abu da zai hada masu gudanar da taron sauya tutar Maulud da masu yayen sabbin kuratan soji a waje guda, ko hanya ba za ta hada su ba, in ba don akwai wata manufa ba. 

Sai dai wani abu da ba a yi zato ko tsammani ba, da misalin karfe 12:15 na ranar Asabar din, sai ga wata babbar motar Sojoji ta zo ta sauke wasu dandazon kuratan sojoji dauke da makamai tare da akwatun harsashi, a daidai gaban Husainiyyah Baqiyyatullah. Wannan abin ya yi matukar ba ‘yan uwan da ke wajen mamaki, har suka yi kokarin tuntubar sojojin dalilin da ya sa aka kawo su gaban Husainiyyah a daidai wannan lokacin, amma sai sojojin kawai suka fara harbi a sama a matsayin amsar wannan tambayar. Daga baya ma sai suka fara kewaye wajen suna harbi. Sai ‘yan uwa suka ba kansu kariya ta hanyar matsar da su daga gaban Husainiyyar da kabbarori da neman taimakon Ubangiji.

Bayan kamar awa guda da faruwar wannan lamari ne, misalin karfe daya saura na rana, sai ga tawagar Janaral Buratai ta biyo ta wajen Husainiyyar da sunan za ta wuce. Kai ka ce tawagar ta shugaban rundunar sojojin Nijeriya sam ba ta san da hatsaniyar da ke faruwa a wannan wajen ‘yan mintoci da suka gabata ba, wanda a ka’idar tsaro, abin zai tilasta musu hakura da fasa bin hanyar, da bin wata hanyar da babu kowane irin barazana a tattare da ita, in har ba wani nufi suke da shi ba.

Zuwansu, tare da masu daukar hotuna cikin kakin sojoji, sai suka shirya wani abu kamar wasan kwaikwayo. Suka yi fuska, tare da nuna rashin sanin faruwar wani abu da wasu kuratan sojoji suka gabatar a wajen kafin zuwansu. A yayin da wasu ‘yan uwa suka tunkare su don su ji ko da me suka sake dawowa wajen za su yi? Sai wasu jami’an tsaro a cikin rigar ‘yan uwa Musulmi (kamar yadda shugaban DSS na Zariya ya bayyana a gaban JCI, cewa akwai mutanen su a cikin ‘yan uwa a wannan ranar a Husainiyyar) suka rika ihu, tare da daddaga sanduna ga sojojin. Nan take sojojin suka bude wuta kan mai uwa-da-wabi.

Bayan bude wutan, tawagar ta Buratai ta wuce, sai wadancan kuratan sojojin da aka kawo da farko suka cigaba da kewaye Husainiyyah, aka rika karo musu karfi. A yayin da suka bi suka kwashe gawarwakin wadanda suka harba, suka saka su a mota suka tafi da su barikinsu. A shirin rana na sashen Hausa a BBC, ‘yan awanni bayan hakan, sai ga hirar kakakin rundunar soja na wancan lokacin Sani Usman Kukasheka, inda yake bayyana cewa, an yi kwanton-bauna ga shugaban rundunar sojoji ne, har ma ya tsallake rijiya da baya. Zargin da nan take shugaban bangaren yada labarai na Harkar Musulunci a wancan lokacin, Malam Ibrahim Usman ya musanta.

Kamar yadda ta bayyana a cikin cikakken bidiyon wannan harin da Harka Musulunci ta sake daga baya, wanda ke da tsawon awanni, Sojoji sun ci gaba da kewaye Husainiyyah, tare da harbin duk wanda suka samu a kewayenta, har zuwa karfe 5 na yamma, lokacin da gwamnan Kaduna, Nasiru Ahmad El-rufa’i ya zo wajen Husainiyyar. Bayan magana da ya yi da jagororin sojin, sai ya yi gaba. Wucewarsa ke da wuya sojoji suka kara tsananta harbe-harbe a Husainiyyar, tare da yunkurin shiga cikinta ta kowane hali don su rusa ta.

Ana cikin wannan halin har dare ya shiga, da misalin karfe 10:30 na dare, sai ga wasu sojojin sun kawo hari gidan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da ke unguwar Gyallesu, kilo-mita kusan biyar daga Husainiyyah Baqiyyatullah. Zuwan su ke da wuya suka yi burki a daidai ginin Banaden, kan kwanar layin da zai kai ka gidan Shaikh Zakzaky, suka jefa wani abin fashewa a wani shago, bayan wuta ta kama sai suka rika amfani da hasken wutan da ke ci wajen saitowa da harbe duk wanda suka gani a kan wannan layin.

Sojoji sun kwana suna harbi a wannan ranar Asabar 12 ga Disambar 2015 din, har zuwa wayewar garin Lahadi, inda suka yi nasarar kashe duk wani mutum da ke gidan Shaikh Zakzaky da suka hada maza, mata da kananan yara, tare da jikkata saura. Suka kuma watsa fetur akan gawarwakin ‘yan uwa da kuma wasu ‘yan uwa masu rauni da ake ajiye su a wani gida kusa da gidan Shaikh din, suka banka musu wuta suka kone kurmus. 

Sannan suka tattaro gawarwakin wadanda suka kashe akan layi, suka tara su waje guda, suka ba mutanen unguwa damar su caje aljihunsu su sace abin da suke so daga jikin gawarwakin. Mutane, ba tare da tausayawa ba, suka rika lalube aljihun gawarwakin ‘yan’uwa suna sace kudaden jiki, da takalma, da zobuna a hannaye.

Da asubahin wannan ranar Lahadin, rundunar ta tura wasu sojojinta zuwa Darur-Rahma, wanda ke tare da gine-ginen tarihi da aka yi su don yin fim din tarihin rayuwar Shehu Usman bin Fodiye (RH) da sauran fima-fiman addini, da kuma masallacin da aka gina na miliyoyin kudi a wajen, tare da makabartan Shahidai. Da yake babu ‘yan uwa a wajen sosai, sun iya kashe wasu daga wadanda suka tarar a nan, suka kama wasu bayan sun raunata su da harbin bindiga, daga bisani suka banka ma wajen wuta, suka rusa shi.

Bincikenmu ya nuna sun je Darur Rahma da tunanin ko Shaikh Zakzaky yana can ne ba ya gidansa, tunda a ranar Asabar bayan sun kewaye Husainiyyah sun samu labarin Shaikh din ya fita ya je Darur Rahma don ziyarar kabarin ‘ya’yansa da sauran Shahidan da ke muhallin. Don haka, ta yiwu ba su gamsu da cewa ya koma gida ba a lokacin.

A daidai sadda suke wannan Ta’addancin a Gyallesu da Darur-Rahma, sun rika harba gurneti akan ginin Husainiyyah, har suka samu dama suka shiga ciki, suka kashe da dama daga ‘yan uwan da ke ciki, wadanda mafi yawa mata ne da kuma kananan yara da suka je a ranar Asabar da safe don yin ‘lesson’ din da suka saba, suka harbi wasu sannan suka kama su suka wurga a motoci suka tafi da su. Bayan nan suka rusa ginin Husainiyyar bakidaya.

Duk da wutar da suka kunnawa gidan Jagora (H) alhali yana ciki, amma Shaikh Zakzaky (H) bai fito ya mika musu wuya kamar yadda suka saka lasifika suna kiransa da ya yi hakan ba, gidan ya kwana yana ci da wutar da suka kunna, a yayin da ba su samu ganinsa ba sai a ranar Litinin 14/12/2015, bayan sun rika saka sifika suna yekuwar cewa yau sun gama da Shi’a, soja na ihu yana cewa: “Al-Zakzaky ka fito ka yi saranda ko mu yi maka kisan wulakanci!.” Da sauran izgilanci ga Allah Ta’ala da Annabi da A’immatu Ahlulbaiti (AS).

Bayan sun shiga cikin konannen gidan, sun balle kofar dakin da Shehin Malamin, iyalansa da wasu almajiransa suke ciki, dukkansu ba su wuce mutum 12 ba, sojojin suka yi musu ruwan wuta, harsasai suka rika zuba a kansu, nan take suka yi wa matarsa jina-jina da harsasai a kirjinta, suka kashe ‘ya’yan Shaikh Zakzaky guda uku, suka harbe shi a hannun hagunsa, da kafarsa ta dama da kuma idanunsa guda biyu, har sai da kwayar idonsa na hagu ta fito waje. Sannan suka fitar da wadanda suka rage a cikin dakin, wadanda mata ne, suka cire musu hijabi, suka daddaure hannayensu da shi, suka kuma ja gangar jikin Shaikh Zakzaky (H) a kasa kan jinin ‘ya’ya da almajiransa, suka fitar da shi kofar gida.

Shaikh Zakzaky (H) ya bayyana a wata hirar da ya yi da babban dansa, Sayyid Muhammad ta wayar tarho daga inda ake tsare da shi a Abuja, cewa: “Mu aka kawo ma hari, aka bude mana wuta, aka harbe mu da bindiga, aka kashe mutane sama da dubu ciki har da ‘ya’yanmu. Ni da matata an harbe mu, ni an ja ni a kan gawar ‘ya’yana ne. Sannan kuma aka kawo mu nan aka kulle duk cikarmu da harsasai a jikinmu. Yanzu haka muna fama da ciwo duk jikinmu da harsasai.”

Bayan sun fitar da Shaikh Zakzaky (H) daga gidan, jikinsa da fuskarsa jina-jina da harsasai, suka saka shi a ‘wheel-barrow’ suna iface-iface da sunan sun kawo karshen Shi’a. Daga baya suka dauke shi suka jefa shi a motar da suka dauki gawarwakin ‘yan uwa suka tafi da shi barikinsu na ‘Depot’ da ke Zariya.

Can da yamma a rannar Litini din suka dauke shi suka wuce da shi Kaduna, inda suka kai shi asibitin 44 da nufin a ceto ransa, bayan da ta bayyana musu cewa bai rasu ba, kuma suna ganin rashinsa a daidai lokacin a matsayin babbar barazana a gare su, bisa wani nufi na Allah Ta’ala.

A asibitin 44 aka yi wa Shaikh Zakzaky (H) da matarsa aiki, aka yi masa daurin karaya (POP) a hannu da kafarsa da sojoji suka karya masa su da harsasai. Sannan a ranar Talata 15/12/2015 suka wuce da su asibitin DSS a birnin Abuja. Daga nan kuma ranar Asabar 19/12/2015 suka tafi da Shaikh din wani asibitin ido a Lagos, inda aka yi masa aikin idon da suka fasa masa.

Bayan kwanaki da aikin idon na Shaikh Zakzaky ne suka maido da shi asibitin DSS a Abuja, inda suka cigaba da tsare su a nan wajen tsawon watanni uku, har zuwa watan Maris din shekarar 2016 sannan suka dauke su daga asibitin suka mai da su wani gida da ke karkashin tsaron DSS a unguwar Maitama a cikin garin Abuja, inda nan ma suka tsare su na tsawon watanni kamar tara. A watan Disambar 2016 suka dauke su daga gidan suka mai da su unguwar jami’an DSS suka cigaba da tsare su.

Sun cigaba da tsare Shaikh Zakzaky a wannan muhallin har zuwa watan Mayun 2018 sannan aka dauko su da matarsa Zeenah aka mai da su garin Kaduna cikin halin tsanantawa da kuntatawa, inda aka gurfanar da su a gaban wata kotu, a yayin da aka tsare su a wani gidan DSS da ke unguwar Rimi Kaduna tun daga watan Mayun 2018 har zuwa Junairun 2020, sannan aka kuma mai da su gidan kurkukun Kaduna inda aka cigaba da tsare su har zuwa ranar 28 ga watan Yulin 2021 da Allah Ya kaddara fitowarsu, bayan kotun ta wanke su daga dukkan tuhumomin da gwamnati ke musu, ta sake su ba tare da wani sharadi ba. 

Kisan-kiyashin Zariya ya yi sanadiyyar kashe ‘yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky (H) fiye da mutum 1000, tare da jikkata daruruwa, ciki har da wadanda sojoji suka kona su da ransu, fatar jikinsu ya salbe, Allah bai nufi kwanansu ya kare a sannan ba. A kisan kiyashin Zaria an shafe iyalai da dama da suka hada uwa, uba da ‘ya’yansu. Ya kuma ci rayukan tsofaffi, da kananan yara, da mata, da samari, da daliban manyan jami’o’i da sauransu.

Yayin da waki’ar ta yi sanadiyyar shafe iyalai daban-daban daga samuwa. Daga ciki akwai Dr. Mustapha Umar Sa’id da ‘ya’yansa uku, duk sojoji sun shahadantar da su a wannan harin. Haka ma ‘ya’ya biyar na gidan Engr. Yahya Gilima, da kuma Malam Yakubu Okene tare da ‘ya’yansa uku. Malam Abdullahi Abbas da ‘ya’yansa shida maza reras matasa. ‘Ya’yan Dr. Isa Waziri su hudu, da iyalan Malam Abubakar Zaki su hudu duk sojoji sun kashe su a yayin wannan waqi’ar.

Amare da dama da ba su fi watanni da aure ba, gami da sauran mata sun rasa mazajensu, haka ma wasu mazajen da suka rasa matayensu. Da dimbin marayun da suka rasa iyaye. Yayin da bayan waqi’ar kuma Gwamnan Kaduna Elrufa’i ya hada kai da sojojin wajen bin duk wani gini da ke da alaka da Shaikh Zakzaky (H) suka rusa shi. Kamar gidan Shaikh din a Gyallesu, da Husainiyyah Baqiyatullah, da Darur-Rahma, da Cibiyar Fudiyyah Center a unguwar Dan-magaji, da kuma gidan da aka bisne mahaifiyar Shaikh Zakzaky a cikin Zariya.

Har ila yau, a tsawon shekaru shida da wani abu da gwamnatin Buhari ta shafe tana tsare da Shaikh Zakzaky, ‘yan uwa sun rika fitowa Muzaharar Allah wadai da tsare shi, tare da kira a sake shi, inda a lokakuta daban-daban a garuruwa daban-daban, musamman a Abuja da Kaduna, jami’an tsaron Nijeriya suka rika budewa masu Muzaharar wuta, sun kashe ‘yan uwa kimamin 200 a tsawon wannan lokacin.

Yanzu haka, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da maidakinsa Malama Zeenah Ibrahim sun samu ‘yancinsu tun a watan Yulin 2021. A farkon watan Octoban 2023 ne suka isa Jamhuriyar Musulunci ta Iran don samun kulawar kwararrun likitoci daga jinyar da suka shafe shekaru suna fama da shi na dirar musu da sojojin suka yi da tsare su cikin rashin kulawa.

Har zuwa yanzu, akwai kimanin ‘yan’uwa Musulmi 50 da gwamnatin Nijeriya ke daure da su a kurkukun Kuje, Abuja, tun bayan da jami’an tsaro suka kama su a yayin wata Muzaharar kira a saki Shaikh Zakzaky a shekarar 2019 a tsakiyar birnin Abuja.

Mafi yawan masu hannu a kisan-kiyashin Zariya, da masu goyon bayan kisan-kiyashin, izuwa yanzu, daga wadanda suka sauka daga mukamin siyasar da suke kai, sai wadanda suka yi ritaya daga aikin tsaro, sai kuma wadanda suka mutu suka fara girban hakikanin sakamakon aikinsu.

An wallafa cikakkun bayanai a littafai daban-daban dangane da waki’ar Zariya, daga lissafan akwai “Kisan-Kiyashin Zariya da Abubuwan da suka biyo bayanta” na Cibiyar Wallafa; da kuma “Haramtacciyar Shari’a” na Cibiyar Wallafa; da “Muhimman Ranaku 200 a Tarihin Harkar Musulunci” na Cibiyar Wallafa; da “Kisan-Kiyashin Zariya Daga Ganau ba Jiyau ba” na Ibrahim Musa, da sauransu.

— Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H)
Website: www.cibiyarwallafa.org
Email: cibiyarwallafa@gmail.com
12/12/2023

Post a Comment

0 Comments