Dakarun Hamas sun ce sun yi wa sojojin Isra'ila 15 kwanton-bauna.

Dakarun Hamas sun ce sun yi wa sojojin Isra'ila 15 kwanton-bauna.
Isra’ila ta ce an raunata sojojinta 619 a kasa da wata biyu

Rundunar Sojin Isra’ila a ranar Laraba ta sanar da cewa akwai dakarunta 19 da suka samu rauni a yakin da take yi a Gaza a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta ce adadin sojojinta da Isra’ilar ta raunata tun bayan da Isra’ilar ta soma kai hari ta kasa a Gaza a ranar 27 ga watan Oktoba sun kai 619.

Ta bayyana cewa daga cikin sojojin nata da aka raunata, akwai wasu 139 da ke cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai.

Dakarun Hamas sun ce sun yi wa sojojin Isra'ila 15 kwanton-bauna

Dakarun Hamas sun bayyana cewa sun yi wa sojojin Isra’ila 15 kwanton bauna, kamar yadda suka bayyana a wata sanarwa.

Duk da sanarwar ba ta yi karin bayani kan sojojin da suka jikkata ba, amma ta tabbatar da cewa akwai wasu da suka rasa ransu.

Wannan na zuwa ne bayan sojojin na Isra’ila a safiyar Laraba sun sanar da cewa an kashe musu mutum goma a Gaza a cikin sa’o’i 24.

Post a Comment

0 Comments