Duniya na dab da ware Isra'ila yayin da take ci gaba da hare-hare a Gaza: Erdogan

Duniya na dab da ware Isra'ila yayin da take ci gaba da hare-hare a Gaza: Erdogan.



Shugaban Kasar Turkiyya Erdogan

"Lokaci ya sauya," in ji Shugaba Erdogan na Turkiyya, yana mai jaddada cewa ra'ayin duniya na komawa kan Isra'ila yayin da kasashe da dama ke daukar matsaya kan ta'asar da take yi a Gaza.


 Isra'ila na fuskantar wariya daga Æ™asashen duniya a yayin da take ci gaba da kai hare-hare ba Æ™aƙƙautawa a kan FalasÉ—inawa, kuma lamarin zai ta'azzara a kwanaki masu zuwa, a cewar Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.


Da yake magana da manema labarai bayan idar da sallar Juma'a a Istanbul, Erdogan ya bayyana cewa "a yanzu ba a tsammanin samun wani kyakkyawan fata daga Isra'ila," amma ra'ayin ƙasashen duniya a kan manufar Tel Aviv ya sauya.


Da yake tuno da batun kaɗa ƙuri'ar jin ra'ayi ta Babban Taron Majalisar DInkin Duniya na farko kan abin da Isra'ila ke yi a yankin Gaza na Falasdinu, Erdogan ya tuna yadda ƙasashe 121 suka ƙi goyon bayan Isra'ila, yayin da 40 suka ƙaurace, sai 10 da suka haɗa da Amurka suka goyi bayan Tel Aviv.


"Amma yanzu lokacin ya sauya," ya ƙara da cewa, yana mai bayyana cewa ana samun ƙarin ƙasashen da ke juya wa Isra'ila baya, inda ya ce: "Hakan na nuna cewa Isra'ila a yanzu tana fuskantar wariya. A kwanaki masu zuwa, za ta sake ganin wannan wariyar fiye da yanzu."


Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai ta sama da ta ƙasa a Zirin Gaza, ta kuma ƙaƙaba mata ƙawanya, tare da kai farmaki ta ƙasa sakamakon harin ba-zata da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.


Akalla Falasdinawa 18,787 aka kashe tun daga lokacin, kusan 51,000 suka jikkata a harin da Isra’ila ta kai, a cewar hukumomin lafiya na Gaza.


Wayar Shugaba Erdogan da Biden


Erdogan ya kuma yi magana game da wayar da ya yi da shugaban Amurka Joe Biden a ranar Alhamis, inda suka tattauna sosai kan abubuwan da ke faruwa a Gaza.


Erdogan ya shaida wa Biden cewa yanzu ne lokacin da Amurka za ta shiga tsakani ta tabbatar da tsagaita wuta.


Dangane da sayar da jiragen yaƙin na F-16 da Amurka ta yi wa Turkiyya, Erdogan ya ce Biden ya shaida masa cewa yana da ra'ayi mai kyau a kan lamarin kuma a shirye yake ya gabatar da shawararsa ga Majalisa.


Bayan wani tsari mai tsawo don sayen sabon samfuran F-16 da kayan inganta tsofaffin samfura, Erdogan ya ba da shawarar cewa Turkiyya da Amurka sun amince da sayar da F-16 da neman zama mambobin NATO na Sweden a lokaci guda.

Post a Comment

0 Comments