ECOWAS ta gindaya sharuda na cire wa Nijar takunkumai

 ECOWAS ta gindaya sharuda na cire wa Nijar takunkumai

ECOWAS ta ce idan sojojin Nijar suka gaza bin ka'idojin da shugabannin kasashen uku da ke kwamitin suka ba su, ba za a cire wa kasar takunkumai ba kuma za a duba yiwuwar amfani da karfin soji.

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta nada kwamiti na shugabanni uku da zai tattauna da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar kan mayar da mulki hannun farar-hula sannan ya duba yiwuwar janye takunkuman da aka kakaba wa kasar.

Shugabannin kungiyar ta ECOWAS sun bayyana haka ne a sanarwar da suka fitar bayan taronsu na shekara-shekara a Abuja ranar Lahadi.

ECOWAS ta nada kwamitin shugabannin kasashen Togo, Saliyo da Benin domin tattaunawa da sojojin Nijar don su amince "da jadawalin mika mulki a dan kankanen lokaci" sannan su "gaggauta dawo da tsarin mulki".

"Za a rika janye tankunkuman da aka sanya wa Nijar ne daki-daki bisa la'akari da sakamakon tattaunawar da kwamitin shugabannin kasashen ya yi da sojojin na Nijar," in ji ECOWAS.

ECOWAS ta ce idan sojojin Nijar suka gaza bin ka'idojin da shugabannin kasashen uku da ke kwamitin suka ba su, ba za a cire wa kasar takunkumai ba kuma za a duba yiwuwar amfani da karfin soji.

Tun da farko, shugaban Nijeriya Bola Tinubu, wanda kuma shi ne shugaban ECOWAS, ya ce kungiyarsu za ta yi kokarin tattaunawa da kasashen da ke karkashin mulkin soji domin mayar da mulki hannun farar-hula "a lokaci kankane".

Post a Comment

0 Comments