Gomman sojojin Isra'ila 'sun kamu' da cututtuka a Gaza.

 Gomman sojojin Isra'ila 'sun kamu' da cututtuka a Gaza.



Ana zargin gomman sojojin Isra’ila wadanda aka jibge kusa da Zirin Gaza da kamuwa da wata cutar fata mai suna leishmaniasis, kamar yadda wata jaridar Isra’ila ta bayyana a ranar Lahadi.


Jaridar ta bayyana cewa akwai sojoji da dama da aka aika da su domin yi musu gwaji, duk da cewa har zuwa yanzu sakamakon gwajin bai fito ba, inda wasu tuni aka aika da su sashen kula da fata domin yi musu magani.


Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin na Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a cikin Zirin Gaza inda suke kashe yara da mata.

Post a Comment

0 Comments