Gwagwarmaya da nasararta a Gazza, israila ta wargaje wasu ne ke tallafe da ita.

Gwagwarmaya da nasararta a Gazza, israila ta wargaje wasu ne ke tallafe da ita.


Daga Nasir Isa Ali.

Zan fara ne da yin shimfida da wata magana wacce Sir. Julius Sallo Malema yayi a wajen wani gangamin da suka shirya domin nuna goyon bayan su ga Falastinawa.

Sir, Malema ya bayyana cewar su mutanen Afirka ta Kudu sune suka fi kowa fahimtar halin da Falastinawa ke ciki, domin su ma sun fuskanci irin wannan halin a hannun Ingila a baya. Ya bayyana cewar yadda suka kwaci kansu a hannun Ingila, hakq yake da yakinin cewar Falastinawa zasu kwaci kansu daga mamayar yan mulkin mallakar da suke ciki a hqlin yanzun.


Bayahuden nan mai fashin baki wa gidan talbijin din israila (Channel 13) Amir Avivie ya bayyana cewar, maganar da janar Hussain Salami yayi a kan sojojin Israila da halin da suke ciki tabbas haka lamarin yake, kuma ya yarda.

Janar Hussain Salami ya bayyana wa masu ruwa da tsaki na ma'aikatar harkokin kasashen waje na Iran çewar, "Kafatanin sojojin Israila suna filin daga, mafiya yawansu suna tunkarar Hamas da Jihadul Islamy a Gazza, da kuma Hizbullah a arewaci da kuma yankin kogin Jodan. Don haka babu ragowar sojojin Israila a tsakiyar kasar in banda yan sa-kai da yan sanda.


Janar din ya kara da cewar, yanzu haka dakarun Huthy dake Yemen sun dakile shigowa da fitar duk wasu jiragen Israila ko masu alaka da ita Israilar. Yacce wannan ya dakile kaso mai yawa na hanyoyin da israila ke samun taimako masu yawan gaske ta ruwa. Kuma matakin na Huthy yana gurguntar da tattalin arzikin israila sosai. Wannan aikin na Huthy tabbas zai ci gaba, kuma zai kara fadada sosai domin samun damar dakile wasu da dama.


Janar din ya kara da cewar kungiyoyin gwagwarmayar musulunci a Iraki da Syria suna kai wa duk wani sansanin sojan Amurka mai alaka da Israila hare hare domin dakile duk wani taimakon da zasu iya kai wa ga Israila daga sansanin na Amurka.

Hakan yana faruwa ne a dai dai lokacin da su kuma yan Gwagwarmaya suke kara tsayawa bisa kan kafarsu suna yin yaki da duk wani kumaji da kwarewa, sannan suna kara fahimtar Lagwan israila sannan suna kara kwarewa ta fannin dubarun yaki daban daban.


Janar Hussain Salami ya kara da cewar, yanzu haka israila a wargaje take wasu ne kawai suka shigo suke tallafe da ita, suma da sannu zasu saketa ta fadi. Wannan Tufanul Aqsa din ya nunawa duniya ko wacece israila, sannan ya nuna irin raunin da tayi, domin a baya tana iya yin yakin da kanta, amma yanzu kam ta gaza yin komai da kanta har wasu ne ke shigowa suna yi mata yakin. Wannan hatta su yahudawan sun fahimci irin girman runin israila, kuma sun fahimcicewar israila ba wajen zamansu bace.


Amour Avivie ya bayyana cewar lallai halin da sojan israila suke ciki ya munana ainun, kuma duk abin da aka ji ya fito daga bakin Salami to lalai hakikanin zancen kenan. Don haka wajibi ne ayi wani abu cikin gaggawa domin kare israila, amma in ba haka ba yahudawa zasu koma suna yawo a duniya kamar yadda suke yi kafin yakin WW2.


Daya daga cikin jiga jigan bangaren siyasa a kungiyar Hamas Dr. Bissam ya bayyana a wata hirar da aka yi da shi a tashar Manar cewar, nasarar da suke samu kan israila ba zata kirgu ba, domin kullum suna ganin sabbin nasararo suna bayyana a garesu.

Ya kara da cewar, duk wani dan israila mace ko namiji wanda ya haura shekara 17 zuwa 30 duk cikarsu sojoji ne, ko dai suna filin daga yanzu haka ko kuma suna zaune suna jiran a kirasu zuwa fagen fama, ko kuma wani aikin na daban.

Don haka duk bayahuden da aka kashe tsaknin wadannan shekaru to soja aka kashe, amma ba farar hula ba.


Yace koma bayan abin da Israilar take yi, wanda idan ta kashe Falastinawa 100 to kusan dukkaninsu fararen hula ne da suka hada da tsaffi, mata yara da kuma masu ayyukan ceton.

Don haka kullum mu muna samun masu rokon mu da cewar a kai su filin yaki domin su yaki israila, yayin da su kuma sojojin Israila ke kin zuwa Gazza yin yaki ko kuma suke tserewa suna barin ayyukan nasu.


Dr. Bissam ya kara da cewar, duk duniya ana goyon bayana Gazza da Falastinu, sannan kuma kullum muna kara samun masu shigar mana yakin a fili kamar Yemen, Syria, Iraq da kuma Lubnan. 

Yayin da ita kuma israila wasu kashen ke yanke duk wata hurda da israila, sannan duk masu taimakon su suna yi ne boye sosai, sawa'un kasashen larabawa ko na turawa.

Post a Comment

0 Comments