Gwagwarmayar sarkin Musulmi Attahiru I da Turawan Mulkin Mallaka kashi na biyu.

 Gwagwarmayar sarkin Musulmi Attahiru I da Turawan Mulkin Mallaka kashi na biyu.



Tarihi ya nuna cewa kafin ya tafi an buga yekuwa cewa sultan Attahiru zai yi hijira mai so ya bi shi, to ya yi harama. Sun bar sakkwato ba guzuri. Ba tanadi, kuma ba shiri, ba takamaiman Ina za’a. Marubucin turawa Muffet ya rubuta cewa da farko turawa sun yi murna da hijirarsa, suna ganin cewa wani dan tawaye zai bar musu kasar su wala, daga baya suka sauya matsaya bisa ga wasu abubuwan da suka ji, suka kuma lura dasu. Duk garin da sultan ya ratsa da jama’ansa mafi yawancin majiya karfin garin binsa suke, wasu yankunan ma yakan tafi da kananan garuruwa baki daya. Wani bature ya rubuta cewa “na gan su cikin kunci, da gajiyawa, kuma a wahale, amma suna da karfin zuciya”. Turawa sun samu rahoton cewa Sultan yana hada jama’a majiya karfi tare dashi, kuma a shirye suke su mutu saboda shi.


Sukaji labarin cewa a maimakon hijira da yayi niya zuwa Makka yanzu so yake ya samu guri ya kafa sansani, ya fara aiwatar da yakin sari-ka-noke. Turawan Ingila sunsan kalar wahalar da suka sha daga irin wannan yakin a Sudan daga Muhammad Al’mahdi, sai suka tsorata, Muffet ya fada a littafin BRABE CAPTAINS cewa, sai turawa suka yi gargadi da tsorata duk wani sarki daya bari sultan ya tafi da jama’ar garin sa inya ratsa. Ko kuma ya bari aka ba shi wani taimako. Su makircinsu suna ganin ko wannan zai karya masa zuciya.


Amman sam bai saduda ba duk inda ya ratsa sai yayi masu nasiha da wajibcin samun hujja a gaban Allah a kan duk wani mataki da zan su dauka na tsayawa ko bin su. Da turawa suka ga makircin baiyi nasara ba sai suka dunga tura sojoji sunayim jama’arsa kwanton 6auna. Amman turawa da kansu sukace duk wani lam6o da zasuyi sukai ma rundunar Attahiru hari sune suke kwasar kashinsu a hannu wani soja yace “suna zama kamar ba mutane ba a yayin da aka kai masu mafarki, masu kai farmakin ne ke yin Asara” wanna dalilin ne turawa suka bada shawarar tura soja masu yawa a yankin Bormi domin a hana shi gaba ko baya.


Haka kuwa akai domin sun rabama sultan hankali wasu sojojin suna kai farmaki suna kwantar 6auna wasu kuma ana Kaisu inda akeso a mashi kofar rago.


Sun isa Bormi cikin gajiya saboda nisan tafiya gashi kuma ana yi ana fada a nan da can. Ga yunwa saboda Karancin Abinci, domin duk garin da zasu zo kafin suzo sai sojan turawa sun rugasu sun tsorata jama’a a kan karsu bi sultan kuma kar su basu gudummuwar abinci in kuma suka sa6a sojan turawa kan yi masu 6arna mai muni.


Zanci gaba insha Allah…….


©️Imamu Mahadi Umar✍🏻

Post a Comment

0 Comments