Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Radda Ya Jajantawa Gwamnatin Kaduna Kan Kisan Fararen Hula a Tudun Biri

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Radda Ya Jajantawa Gwamnatin Kaduna Kan Kisan Fararen Hula a Tudun Biri
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya jajantawa takwaransa na jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, da gwamnatin jihar Kaduna, da iyalan wadanda abin ya shafa, da daukacin al’ummar jihar bisa harin da jiragen yaki da sojoji suka kai a makon da ya gabata wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama a garin Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Gwamna Radda wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Hon. Jabiru Tsauri, a ziyarar da ya kai wa Gwamna Uba Sani a gidan Sir Kashim dake Kaduna a ranar 11 ga watan Disamba 2023 ya bayyana lamarin a matsayin abin ban takaici, yana mai yi wa al’ummar jihar Kaduna jajen wannan ibtila’i da ya fada masu a madadin Gwamnatin Jihar Katsina.

Tawagar jihar Katsina karkashin jagorancin Hon. Jabiru Tsauri sun hada da kwamishinan kasafi da tsare-tsare na tattalin arziki Hon Bello Hussain Kagara; Kwamishinan harkokin addini, Hon Ishaq Shehu Dabai; Mai ba da shawara na musamman kan harkokin wasanni da raya karkara, Hon Abubakar Tsanni da mai ba da shawara na musamman kan tattalin arzikin karkara, Eng Yakubu Nuhu Danja.

Isah Miqdad
SSA Digital Media
11/12/2023

Post a Comment

0 Comments