Gwamnan Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD ya kara kudin ciyar da daliban makarantun kwana "Boarding Schools"

 Gwamnan Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD ya kara kudin ciyar da daliban makarantun kwana "Boarding Schools"



Mai Girma Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD ya amince da a kara yawan kudin da ake ciyar da daliban da ke makarantun kwana na jihar. A da dai, duk dalibi ana ciyar da shi kan kudi Naira 100, amma yanzu Mai Girma Gwamna ya mayar da su Naira 270. Wannan matakin ya sa gwamnati ta ware kudi Naira N355,773,600 domin sayo kayan abinci ga daliban makarantun kwana su 10,862 da ake da su.


Matakin gwamnati na da nufin inganta kudaden ciyar da daliban bayan da gwamnati ta gano yadda farashin kayan abinci ya yi a duk kasa bakidaya. Wannan ne dai karon farko da aka samu karin yawan kudin ciyar da daliban makarantun kwana karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda PhD a matsayin Gwamnan jihar Katsina.


Isah Miqdad

SSA Digital Media

8/12/2023


Kungiyar People Enlightenment Forum ta shirya taron fadakarwa kan illilon ta’ammali da miyagun kwayoyi ga matasa a jihar katsina.





Post a Comment

0 Comments