Gwamnatin jihar Katsina zata ƙwace dukkan filayen gandun dajin da aka raba ba bisa ka'ida ba.

 Gwamnatin jihar Katsina zata ƙwace dukkan filayen gandun dajin da aka raba ba bisa ka'ida ba. 



Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗda yace gwamnati zata ƙwace dukkanin filayen gandun daji dake hannun mutane da aka raba ba bisa ka'ida ba


Gwamnan ya bayyana hakan jim kaɗan bayan ya amshi rahoton kwamitin binciken gandun daji da ya ƙaddamar.


Katsina Post ta samu cewa Gwamna Dikko Raɗda a ranar 21 ga watan August ya ƙaddamar da kwamiti na musamman da zai yi binciken ƙwakwaf domin gano illahirin filayen gandun daji waɗanɗa aka raba ba bisa ka'ida ba a faɗin jihar. 


Kwamitin ƙarƙashin jagorancin Alhaji Khalilu Baƙo ya zagaya faɗin dazuzzukan dake a ƙananan hukumomin jihar sannan ya zauna da illahirin masu ruwa da tsaki na ƙananan hukumomin. 


Gwamnan da yake amsar rahoton ya bayyana aniyar sa na ganin ya aiwatar da duk shawarwarin da kwamitin ya gabatar a cikin rahoton nashi. 


Sannan ya yaba ƙoƙarin kwamitin tare da yin godiya akan ayyukan da ya gabatar. 


Tun farko da yake jawabi, shugaban kwamitin ya ce sun samu ziyarartar ƙananan 30 dake faɗin jihar yayin gudanar da binciken.


Shugaban ya ce kwamitin ya shirya rahoto akan gaskiya da amana kamar yanda yayi alƙawari a gaban Gwamnan.


Daga ƙarshe ya gode ma Gwamna Raɗɗa da ya basu damar yin aiki domin ganin an kwato haƙƙin al'ummar jihar Katsina.

Post a Comment

0 Comments