Gwamnatin Saliyo ta yi jana’izar jami’an tsaro 18 da aka kashe a abin da ta kira yunkurin juyin mulkin da wasu suka yi a makon jiya.

 An yi jana’izar sojojin da aka kashe a yunkurin juyin mulki a Sierra Leone



Da sanyin safiyar ranar 26 ga watan nan na Nuwamba ne, wasu dauke da makamai suka kai hari a rundunar soji da barikin soji biyu da gidajen yari biyu da manyan ofisoshin ‘yan sanda biyi, inda suka yi gumurzu da jami’an tsaro.

Gwamnatin Saliyo ranar Laraba ta yi jana’izar jami’an tsaro 18 da aka kashe a abin da ta kira yunkurin juyin mulkin da wasu suka yi a makon jiya.


Shugaba Julius Maada Bio ya halarci jana’izar jami’an tsaron da suka hada da sojoji 16 da dan sanda da kuma ganduroba a makabartar soji da ke Freetown, babban birnin kasar.


Iyalan jami’an tsaron sun halarci jana’izar tare da wakilai daga bangaren addinai da sojoji da ‘yan sanda, inda daruruwan mutane suka yi layi a kan titin makabartar domin yin bankwana da mamatan.


Da sanyin safiyar ranar 26 ga watan nan na Nuwamba ne, wasu dauke da makamai suka kai hari a rundunar soji da barikin soji biyu da gidajen yari biyu da manyan ofisoshin ‘yan sanda biyi, inda suka yi gumurzu da jami’an tsaro.


Lamarin ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 21, a cewar Ministan Watsa Labarai na kasar Chernor Bah.


Tun daga lokacin an kama akalla mutum 60 bisa hannu a abin da Shugaba Bio ya bayyana a matsayin yunkurin juyin mulki.


"Yau, muna cike da bakin ciki. Ba kawai muna alhini ba ne, a’a har ma da kasancewa wadanda nauyi ya rataya a wuyansu na karrama gwarazanmu," in ji shugaban kasar.


Ya kara da cewa jami’an tsaron sun yi sadaukar da rayuwarsu domin kare kasarsu daga “azzalumai da ‘yan ta’adda da suka yi barazanar jefa kasarmu cikin bala’i,” yana mai cewa mutuwarsu ba za ta tafi a banza ba.

.

Post a Comment

0 Comments