Halin da yaran Falasdinawa da suka rasa ido sakamakon harbin da Isra'ila ta yi musu ke ciki

 Halin da yaran Falasdinawa da suka rasa ido sakamakon harbin da Isra'ila ta yi musu ke ciki.

Yacce Khaled Dan shekara biyar ya rasa idanunsa a gaban mahaifinsa a Gaza.

Daga FAYHA SHALASH


Rana ce kamar kowacce rana a rayuwar iyalan Malalha da suka fito daga kauyen Bazariya na kusa da Nablus a Yammacin Gabar Kogin Jordan da Yahudawa suka mamaye, amma a cikin dan kankanin lokaci komai ya sauya.



A ranar 23 ga Yuni, Akram Malalha na tuka mota zuwa kasuwa tare da dansa dan shekara biyar, mai suna Khaled.


A yayin da suke wucewa ta babban titin garin, sai suka ji karar harbe-harbe a wata mashigar kauyen - ashe rikici ake yi tsakanin mazauna yankin da sojojin Isra'ila.


Akram bai kula da cewa harsashi ya samu idon dan karamin dansa da ke zaune a kujerar baya ba. Har sai bayan Khaled ya fara rusa kuka da ihu. Mahaifin ya waiwaya inda ya ga fuskar dansa sharkaf da jini.


Akram ya shaida wa TRT World cewa "Lamari ne mummuna. Jini ya baibaye fuska da tufafin Khaled. Ban san ashe alburushi ne ya daki idonsa ba.


Nan da nan na tsayar da motar na je kujerar baya don rarrashin sa. A sannan ne na ga wata babbar huda a jikin gilashin motata, sai na fahimci lallai harsashin da sojojin Isra'ila suka harba ne ya hudo ya same shi."


A wajen iyalin da ma karamin yaron, awannin da suka biyo baya sun zama na bakin ciki, sun kai yaron wani asibiti da ke kusa, sannan aka mayar da shi zuwa Asibitin An-Najah da ke garin Nablus, inda a nan ma likitoci suka ce ba su da kayan aikin da za su duba idon.


A wannan dare, an kai yaron wanda ya riga ya jikkata zuwa Asibitin Hadassah da ke Birnin Kudus, inda likitoci suka bai wa mahaifin mummunan labarin cewa sai dai a cire idon gaba daya don kubutar da rayuwarsa.


Mahaifin ya kara da cewa "Mun zama kamar wasu masu nutsewa da ke fafutukar kubuta, muna ta tunanin me za mu yi don kar Khaled ya rasa idonsa. Amma abun ya zama ya munana ta yadda ba makawa sai dai a cire idon."


Saboda hatsari da wahalar da ke tattare da tiyatar da za a yi masa, an mayar da Khaled zuwa Asibitin Tel Hashomer da ke Tel Aviv. Ya yi nasarar samun kulawa ba tare da jinkiri ba.


Hanyar kai Falasdinawa asibitocin isra'ila na da matukar wahala a yanzu. Akwai Falasdinawa da yawa da suke ta zaman jira a kai su asibiti a Isra'ila, inda suke zaman jira na tsawon lokaci, kwanaki, makonni ko ma watanni kafin su samu a mayar da su can.


Ana yawan sukar asibitocin Isra'ila saboda gallaza wa Falasdinawa marasa lafiya, kuma suna kokarin nuna wa duniya su ba sa nuna bambanci wajen gudanar da ayyukansu, ba sa nuna wariya ga marasa lafiya da ba Falasdinawa ba.


A yawancin lokuta, Falasdinawa da suka samu raunuka na fuskantar matsaloli irin na rashin amincewar jami'an tsaro hana su zuwa asibitocin Isra'ila.


Mazauna Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye na shan wahala sosai saboda dokokin da aka saka kafin mutum ya je asibitin Isra'ila.


Dokar kasa da kasa ta tanadi cewa isra'ila da ta zama shugabar mamaya, dole ta dauki alhakin tabbatar da kula da lafiya da walwalar Falasdinawa.


Wannan ya hada da bayar da damar samun kula da lafiya da tabbatar da sun samu magunguna da ci gaba da kula da su a ko yaushe. Isra'ila za ta samar da yanayin tabbatar da an kai kayan kula da lafiya da magunguna idan Bafalasdine ba shi da lafiya.


Game da batun Khaled, an cire idonsa a Asibitin Tel hashhomer, an saka wata farar kwalba a madadin idon. Yarin ya fuskanci matsananci zafi lokacin tiyatar da bayan an gama.


Amma babbar illar da aka smau ta shafi kwakwalwa - abun da har yanzu ke damun Khaled. A kowacce rana, yana sa mahaifinsa zubar da hawaye a duk lokacin da ya tambayi "Ina son idona ya dawo. Yaushe likitoci za su dawo min da idona?


Akram ya ja dogon numfashi tare da cewa "Yana tambayar ina idonsa yake, ya kuma san sojojin isra'ila ne suka raba shi da shi, amma yana fatan zai dawo."


Wannan yanayi da ya shiga na kara tabarbarewa sakamakon yadda Khaled ya ki bayar da goyon baya ga likitan kwakwalwa. Maimakon haka, sai ya ware kansa. Ba ya son yin wasa, ba ya son ya hau mota tare da babansa.

Post a Comment

0 Comments