Hamas ta ce kawo karshen hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza yana da muhimmanci.

 Hamas ta ce kawo karshen hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza yana da muhimmanci.




Rundunar sojin kungiyar Hamas ta Falasdinu ta bayyana cewa kawo karshen hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza shi suka fi fifitawa, tare da jaddada yin watsi da duk wata yarjejeniyar musaya ko tattaunawa inda har ba a cika wannan sharadi ba.


An bayyana hakan ne a cikin wani jawabin da Abu Ubaida, mai magana da yawun rundunar Al Qassam Brigades ya yi, wanda aka watsa a tashar talabijin ta Aljazeera.


Abu Ubaida ya sanar da cewa mayakan Al Qassam "sun lalata motocin soji fiye da 825, da suka hada da manyan motocin yaƙi da tankokin yaƙi tun farkon mamayar da Isra'ila ta kai ta ƙasa."


Ya ƙara da cewa: "Abin da muka sa a gaba shi ne mu dakatar da kai hare-hare kan al'ummarmu a Gaza, kuma babu wani fifiko da ya wuce haka."


Ya jaddada cewa "ba za mu amince da duk wata yarjejeniyar musaya ko shawarwari ba kafin a daina kai hare-hare kan al'umma

Post a Comment

0 Comments