Hamas ta ce mayakanta sun kashe sojojin Isra'ila 40 cikin awanni 48.

Hamas ta ce mayakanta sun kashe sojojin Isra'ila 40 cikin awanni 48.



Hare-haren da Isra'ila ta kwashe 66 tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 17,997, galibinsu mata da kananan yara sannan fiye da mutum 49,200 sun jikkata kana dubban na binne a karkashin baraguzan gine-gine.

 Hamas ta ce mayakanta sun kashe sojojin Isra'ila 40 cikin awanni 48


Qassam Brigades, wato bangaren aikin soji kungiyar Hamas da ke fafatukar kare 'yancin Falasdinawa, ya sanar da kashe sojojin Isra'ila 40 da lalata motocin sojinsu 44 a awanni 48 da suka wuce.


“A cikin awanni 48 da suka wuce, mayakan Qassam sun lalata motocin soji 44 daga kowacce kusurwa da ake yaki a Gaza,” kamar yadda suka yi karin bayani a manhajarsu ta Telegram.


“Mayakansu sun tabbatar da kashe sojojin Isra'ila 40 sannan sun jikkata gommai,” in ji kungiyar.


Sanarwar ta kara da cewa mayakan sun yi wa sojojin Isra'ila kofar-rago sannan suka lalata wata cibiya yaki ta Isra'ila tare da harba rokoki kan sojojin na Isra'ila.


Isra'ila ba ta fitar da wata sanarwa game da wannan ikirari na Hamas ba.

Post a Comment

0 Comments