HANNUN WAHABIYAWA A KISAN KIYASHIN ZARIYA
Waki’ar Zariya ta auku ne da nufin kawar da Shaikh Ibraheem Zakzaky da Da’awarsa baki-daya. Don haka ma tun kafin aukuwarta da kuma abubuwan da suka biyo baya, sun nuna baro-baro cewa akwai cikakken gudummawar wadanda ake kira Wahabiyawa, wato akwai hannun tushen Wahabiyanci na duniya, gidan sarautan Saudi-Arebiya a cikin duk abin da ya faru din.
A nan, za mu kawo wasu abubuwa guda shida da suka auku kafin da kuma bayan kisan-kiyashin na Zariya wadanda a zahiri suke tabbatar da hannun wahabiyawan, wadanda suke maqiya ne ga Shi’a a kan wannan waki’ar:
1- Rahoton WISAL TV a kan yaduwar Shi’a a Nijeriya.
2- Kashejin Shekau ga Shaikh Zakzaky, da kuma kai hari da sunan Boko Haram.
3- Kisan-Kiyashin Zariya da yabawan sarkin Saudiyyah.
4- Rahoton AL’ARABIYYA a yayin zuwan Buhari Qatar.
5- Rahoton DW na bayanin MBS a kan dakile tasirin Iran a Afirka.
6- Gudummawar Malaman Wahabiyawa/Izala a kan waki’ar.
*Rahoton Tashar WISAL TV:
Watanni kamar uku kafin aukuwar waki’ar Zariya, a cikin watan Satumbar 2015, wani gidan TV mai suna Wisal, mallakin kasar Saudi-Arebiya, sun yi wani ‘documentary’ inda a cikinsa suka nuna hadarin da ke fuskantar Nijeriya na yaduwar Shi’anci da tasirin Iran a tsakanin matasa, ta hannun Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). Inda a karshe suka nuna takaici ga yadda aka kyale hakan na faruwa a kasar da tafi ko ina girma da tattalin arziki a cikin kasashen Afirka.
Rahoton ya bayyana cewa: “A duk duniya, a yanzu babu wata kasa mafi hadari kamar Nijeriya, saboda yadda wata sabuwar fahimta ke yaduwa har ta mamaye jihohi hudu wanda a cikinsu akwai masu wannan akidar kimanin mutane miliyan 25.”
Suka ce: “Wannan cutar da ta bulla a Nijeriya ita ce Shi’a, wacce take yaduwa a tsakanin matasa, wadanda suke makarantun boko suna karantar ilimin likitanci, Kanikanci da wasu fannonin na ilimin boko, wanda kuma ana daukar nauyinsu su je su yi kware a fannoni daban-daban. Wannan ya sa da yawan matasan basu san ilimin addini ba, don haka cutar Shi’anci ke yaduwa da gagawa a tsakanin matasan Nijeriya.”
Suka cigaba da cewa: “Wani matashi mai suna Ibraheem Yaqoub Zakzaky ne ya buya a bayan wasu abubuwa kamar kokarin ‘yanto masallacin Kudus daga hannun Yahudawa da goyon bayan raunanan al’ummar da ake zalunta, yana yaudarar mutanen Nijeriya zuwa ga shiga wannan akidar ta Shi’anci.”
Suka ce: “Malamin wanda aka san shi a matsayin Dan tawaye, ana gayyatarsa ya je Iran don a kara masa ilimi a kan akidar Shi’a. Tsayuwarsa wajen aiki ma Shi’anci ya sa shi da mabiyansa sun kai ga suna shirya wasu Muzaharori kamar na Quds da Ashura. Ya samu nasarar yada wannan cutar ne ta hanyar yin abin da ake kira TAKIYYA, wanda hakan ne yasa jahilai suke binsa.
Da’awarsa ta fara shahara ne a shekarun 1980s, ta kuma cigaba da yaduwa a 1990s. Abin da ya fi bata rai shine yadda Malamai suka kyale, suka yi shiru a yayin da wannan Akidar mai hadari take cigaba da yaduwa.”
Rahoton na Wisal yace: “Zakzaky din, ya yi fice a harkokin Diplomasiyya, ta kai ga yana tura dalibai zuwa jami’ar Tehran a Iran su yi karatu su kware a fannoni, har ma sun fara dawowa Nijeriya suna yada Shi’anci a tsakanin mutane.”
Suka ce: “Suna da wata Jarida da ake kira ALMIZAN, wacce ake buga ta da Hausa, wacce take yaduwa a cikin mutane sosai. Tana taimakawa wajen kara yaduwar Shi’anci. Kuma suna da Website na Hausa da Turanci wanda suke yada manufofinsu. Kuma suna sayan lokaci a gidajen rediyo da talabijin da jaridu, don su yada manufofinsu ga al’umma. Wannan ne ya basu damar samun alaka da kyakkyawar fahimta da masu bin Darikun Sufaye, suke haduwa don su fuskanci Wahabiyawa Ahlussunah.”
Bayan kare rahoton, sai suka saka hira da wani mutum mai suna Dakta Muhammad AlMubarak, inda yake sharhi a kan abin, a ciki yake cewa: “A shekarar 1979, shekarar da Khumaini ya yi juyin juya hali, babu Shi’a ko daya a Afrika. Sam basu san Shi’a ba kwata-kwata. Afirka nahiyar Musulmi ne. Eh, akwai wasu kasashe da mafiya yawan mutanen cikinsu Musulmi ne, akwai kuma wasu da kadan ne Musulmi din, amma Shi’a sam ba a san Shi’a ba a nahiyar baki daya. Haka nan yake a da yawa daga kasashen Musulmi, kamar Indinosia.”
AlMubarak yace: “Amma bayan juyin Khumaini a 1979, sai aka fara aikin yada Akidar Shi’anci zuwa kasashe daban-daban. Za mu iya gani yanzu, abin mamaki, Shi’a ta mamaye mafi girman kasashen Afirka a yawan mutane da tattalin arziki. Yanzu muna jin hauhawan farashin mabiya Shi’a a Nijeriya.”
Wannan rahoton, wanda muke da ‘video clip’ dinsa, in mutum ya nazarce shi zai ga cewa Saudiyya tana jin takaicin yaduwar da’awar Shaikh Ibraheem Zakzaky na Harkar Musulunci da yake yi a tsakanin matasan Nijeriya, wanda kuma suna ma Da’awar kallon Shi’anci ne, saboda ganin cewa Jagoran Harkar da mafiya yawan mabiyansa suna bin Mazhabar Ahlulbait (AS) ne.
Don haka sun nuna a cikin rahoton cewa akwai bukatar takawa yaduwar Shi’ancin birki ta kowane hali, a yayin da suke kokarin nuna cewa Harkar Musulunci din, ko abin da suke kira Shi’anci, na daga cikin tasirin juyin-juya-halin Musulunci ta Iran, wacce Amurka, Isra’ila da ita Saudi-Arebiya din suke tsananin gaba da shi.
*Kashejin Shekau Da Kawo Harin Bom A Kan ‘Yan Uwa:
Ba a jima da yin wannan rahoton na Saudiyyah a kan takaicinsu na yaduwar Shi’anci a Nijeriya ba, kamar wata guda bayan hakan, a karshen watan Octoban 2015, sai ga shugaban wata kungiyar da ke tafiya bisa doron Wahabiyanci da suke kai hare-haren ta’addanci a Arewacin Nijeriya da aka sakawa suna Boko Haram, mai suna Abubakar Shekau yana kasheji ga Shaikh Zakzaky da almajiransa a kan su gaggauta tuba daga Shi’anci.
A cikin garejeren bidiyon wanda ya yadu, har yanzu kuma akwai shi a wayoyin mutane, Abubakar Shekau ya furta cewa: “’Yan Kaduna! Kai Zakzaky! ‘Yan Shi’a, masu TAKIYYA! Ku tuba!”
Ku lura da wasu abubuwa a cikin wannan garejen maganar ta Shekau, ta yadda yake kiran sunan Shaikh Zakzaky gatsai yana cewa ya tuba, alhali a baya Shekau bai taba kama sunan wani Malamin addini a kasar nan ya masa kasheji ba ko ya nemi ya tuba ba.
Kuma ku lura da yadda ya ambaci kalmar TAQIYYA, wannan kalmar da rahoton Wisal TV ya jaddada shi, cewa wai Shaikh Zakzaky na yaudarar matasa ne ta hanyar yin TAKIYYA. Bai zama abin la’akari ba, a yayin da kalmomin Shekau suka dace da na ‘yan rahoton Saudiyya?
To, bayan wannan kashejin kuma da wata guda, har wala yau, a karshen watan Nuwambar 2015 sai aka kawowa ‘yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky harin bom a yayin da suke kan hanyarsu na tattakin juyayin Arba’in din Imam Husaini (AS), daga Kano sun nufo Zariya.
Harin Bom din da ya ci rayukan almajiran Shaikh Zakzaky mutum 23, an yi nasarar dakile tashin na mutum daya, a yayin da na guda daya ne ya tashi ya kashe wannan adadin. Kwatam sai aka ji a kafafen yada labarai, wai Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kawo wannan harin.
Sai ya zama kamar wannan ne ma’anar kashejin Shekau ga Shaikh Zakzaky da ‘yan Shi’a, a yayin da yake cewa su tuba. Da basu tuba ba, suka cigaba da Shi’anci, gashi ya kawo musu harin kunar bakin wake ma.
Sai dai Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky, a yayin da yake jawabi a wajen rufe taron Arba’in, kwana uku bayan aukuwar harin, ya bayyana cewa ba kowa ke da alhakin kawo harin ba face jami’an tsaron Nijeriya, wadanda dama su ke da alhakin duk abubuwan da ke faruwa a kasar nan da sunan rashin tsaro, ciki kuwa har da hare-haren Boko Haram din.
Bayan Shaikh Zakzaky ya dora alhakin harin a kan jami’an tsaron, bisa dalilan da ya bayyana a cikin jawabinsa na ranar Arba’in din, wanda aka gudanar a ranar Alhamis, 3 ga watan Disambar 2015. Ba a samu wata murya daga bangaren gwamnati ko jami’an tsaro da ta musanta zargin da Shaikh Zakzaky ya yi a wannan lokacin ba. Sai kawai martanin da sojoji suka bayar kwanaki tara bayan wannan jawabin, wanda shine ‘Kisan-Kiyashin Zariya’.
*Kisan-Kiyashin Zariya Da Yabawan Sarkin Saudiyya:
Mun riga mun yi bayani a kan waki’ar Zariya tun a babin farko na wannan littafin, kuma mun kawo yadda wata kafar yada labarai ta ‘Fars News Agency’ ta ruwaito cewa a ranar 16/12/2015 kwanaki biyu bayan gama kisan-kiyashin sojoji a Zariya, Sarkin Saudiyya, Salman Ibn Abdul’azeez ya kira shugaban qasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya taya shi murna a kan aikin da ya yin a murqushe Harka Islamiyya da sunan cewa hakan fada ne da ta’addanci.
Sarki Salman, ya bayyana kisan-kiyashin Zariya a matsayin yaki da ta’addanci da murkushe ‘yan ta’adda. Wanda a rahoton Wisal TV da ya gaba za mu iya gane suna nufin tasirin Iran a Afirka da yaduwar Shi’anci ne suke nufi da Ta’addancin, kamar yadda kuma za mu gani a gaba.
*Rahoton AL-ARABIYYA TV a yayin zuwan Buhari Qatar:
Kwatsam sai ga tashar talabijin na AL-ARABIYYA ya yi wani rahoto a kan ziyarar da Shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya kai Qatar, wanda suka dora ‘video’ din rahoton a shafin gidan talabijin din a ranar Talata 1/03/16. Sukai masa take da “Sabon gargadi daga Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, game da masu yada busharar Shi'anci a Afrika.”
Suka ce: “Buhari ya hangi wani hatsari da ke tunkarowa na yaduwar wata Aqida mai hatsari, wacce manufarta ita ce, tayar da fitina, raba kan al'umma da kawo hatsaniya.”
Rahoton yaci gaba da cewa: “Nijeriya wacce take Cibiyar Afrika; ta fi kowace qasa a Nahiyar ta Afirka yawan mutane, wacce ake qiyasta musulmin cikinta sun kai miliyan 85. Daga cikin su akwai qasa da miliyan 10 ‘yan Shi'a, sauran kuma musulmai ne mabiya Sunnah.”
Su cigaba da cewa: “Shi'a ta yadu daga baya (a Nijeriya) ta hannun Ibraheem El-Zakzaky, wanda Iran ta nasabta shi a matsayin wakilin Hizbullah a Nijeriya. Jami'an tsaro sun kama shi ne a watan Disambar shekarar da ta gabata; bayan sun tuhume shi da yunkurin kashe Shugaban Hafsan sojojin Nigeria, a lokacin da yake kan hanyarsa ta wucewa Zariya; wacce ake ganin ta a matsayin wuri mafi muhimmanci ga mabiya Shi'a da suke zaune a Arewacin Nijeriya, kuma nan ne mazaunin Shugabanta da ke samun goyon bayan Iran.”
A nan sai suka sanya bidiyon Buhari yana cewa: “Arangamar ta (ta Zariya) faru ne a lokacin da aka yi kokarin dakatar da tawagar Hafsan-Hafsoshin sojojin Nijeriya. Daga baya Shi'a ta yi karfi. Kuma muna da masaniyar cewa tana samun karfafa da abin da yayi kama da haka daga Iran”.
Sannan suka cigaba da sharhi da cewa: “Shuwagabannin siyasa, da sojojin Nijeriya ra'ayinsu ya zo daya a kan cewa Shi'a a Nijeriya - wacce take da goyon bayan Iran - ra'ayinsu daya da kungiyar Boko Haram, wacce ta yi wa Da'esh bai'a.”
Suka ce: “Dalilai da dama ne suka sabbaba yaduwar Shi'a a Nijeriya, daga cikin su akwai talauci, jahilci, ba da tallafin karatu, (da Shi'a suke badawa) da kuma yaudarar mutane ta hanyar taken 'yanto Masallacin Al-Aqsa. Wadannan dalilan ne ke sa mutane tudadar shiga wannan Mazhabar da Iran ke karfafawa.”
Mai karatu, ka lura da yadda bayanan mutanen nan ke zuwa a tare; yaduwar Shi’anci; tasirin Iran; samun goyon bayan Iran; da batun Takiyya ko taimakon raunana. Wadannan sune duk abin da suke kokarin su nuna cewa Harkar Musulunci karkashin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na samu don habbakarta. Kuma shine abin da suke qoqarin a dakile ta kowace hanya.
Kuma har ila yau, kalaman Buhari ya nuna maka kai tsaye me suka yi a Zariya, sun afkawa Shaikh Zakzaky ne da almajiransa, don su dakile yaduwar tasirin Iran a Afirka, musamman a Nijeriya. Amma ba wani abu wai tare hanya ne ya sabbaba kashe mutum 1,000, da kama Shaikh Zakzaky a daure tsawon shekaru da rauni a jikinsa ba, kamar yadda za mu ji daga bakin yariman Saudiyya a gaba.
*Rahoton DW Rediyo Na Bayanin MBS Kan Kan Daqile Tasirin Iran A Afirka:
Sai aka zo, a ranar 24 ga watan Afrilun 2018, shashen Hausa na gidan rediyon DW da ke Jamus ya fitar da rahoton murya da rubutacce a shafinsa, inda yariman sarkin Saudiyya, Muhammad Bin Salman ya furta a sarari cewa su ke da alhakin harin da aka kaiwa Shaikh Zakzaky a kokarinsu na dakile karfi da tasirin Iran a Afirka!
Rahoton na DW, ya bayyana cewa: “A wata hira da jaridar Times ta Amurka ta yi da yarima mai jiran gado na Saudiyya, Muhammad Bin Salman ya ce kasarsa ta kai gouro ta kai mari a Afirka don ganin ta rage tasirin Iran a nahiyar, yadda ya zuwa yanzu tai nasarar karya karfin kasar ta Iran a Afirka da kimanin kaso 95 cikin 100.”
A shafinsu na yanar gizo, DW, sun rubuta a karkashin wani hoto da suka saka, cewa: “Muhammad Bin Salman ya ce kasarsa (Saudi-Arebiya) ce ta dakushe karfin Ibrahim al-Zakzaky a Najeriya”
Sannan rahoton nasu ya cigaba da cewa: “Dr Zayeed Al-Amri mamba a cibiyar tsara dabarun mulki da tunkarar matsaloli na kasar ta Saudiya ya yi karin bayani kan manufar yariman inda ya ke cewar ‘abun da yarima ke nufi a nan shi ne tun bayan da ya ayyana shirinsa na tunkarar makiya, Saudiya tai nasarar karya tanadin Iran a Yemen da Somaliya da Djibouti da Sudan kamar yadda ta lalata yunkurinta na kafa makamanciyar kungiyar Hizbollah a Nigeriya da hana Ibrahim Zakzaky yin juyin mulki a kasar.”
Kafar ta DW, ta kuma ruwaito Dr. Amani al-Taweel ta cibiyar bincike na Al-Ahram a Masar, inda take cewa: “a gaskiya Saudiya ba abun da ya fi damunta tamkar yada akidar Wahabiyanci a Afirka fiye da kulla huldar kasuwanci da alakar diflomasiyya ta ban gishiri in baka manda.”
A wannan rahoton, Muhammad Bin Salman da sauran masu sharhi sun bayyana karara dalilin kisan kiyashin Zariya, cewa kwangila ce ta gidan Sarautar Saudiyya zuwa ga shugaban Nijeriya da jami’an tsaronta a kan su dakile mata Shaikh Zakzaky da abin da suke kira Shi’anci, a kokarinsu na dakile tasirin Iran a Afirka da kuma karfafar yaduwar Akidarsu ta Wahabiyanci.
* Gudummawar Malaman Wahabiyawa/Izala A Kan Waki’ar:
A can baya mun kawo yadda Malaman Wahabiyawa suka rika zame-zame da gwamnati da kuma yin wasu kalamai na nuna farin cikinsu kafin da kuma musamman ma bayan abin da ya faru na kashe wadanda suke kira ‘yan Shi’a fiye da 1,000 a Zariya.
Mun kawo yadda a ranar Asabar, 19/12/2015 wasu daga cikin Gwamnonin Arewa, karkashin Kasim Shettima, suka gabatar da zama a Kaduna, inda suka tattauna yadda za su bullowa takawa Harkar Musulunci burki a jihohinsu.
Da kuma zaman Kungiyar Limamai da Malamai na jihar Kaduna a ranar 28/12/2015 da suka gana da Nasiru Elrufa’I, inda suka bayyana goyon bayansu a kan fada da yake ‘Yan Shi’a a jihar tasa. Suka kuma bayyana masa cewa hakan da yake wani aiki ne ma addinin Musulunci.
Mun kuwa kawo yadda a 14 ga Junairun 2016, shima GOC I Division, Manjo-Janar Adeniyi ya gana da wasu Malaman Wahabiyawa da Limamansu, ya musu bayani a kan shirin jami’an tsaro a kan Shi’a da kuma gudummawar da ake bukata daga Malaman, har ya basu kyautar dubu 500 su raba.
Mun kawo kuma inda a ranar 21/12/2015, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi, daya daga cikin masu ra’ayin Wahabiyanci ya yi jawabi, inda yake yaba ma sojoji a kan abin da ya suka yi, da sunan hakan taimakon Sunnah ne da magance masu zagin Sahabbai.
Kungiyar Izala, musamman ta bakin shugabanninta, Shaikh Sani Yahaya Jingre, Shaikh Abdullahi Bala Lau da Shaikh Kabiru Gombe sun ta wa’azozi suna masu murna da abin da aka yi a Zariya.
Wani abu da ba mu ambata ba a baya shine bayanin daya daga cikin Malaman Izala, Shaikh Gero Argungun wanda ya yi a fadar sarkin Yawuri, kwanaki kadan bayan kisan-kiyashin na Zariya, inda bayan ya gama yin karairayi ga Shi’a da Shi’anci a karshe ya shiga bayyana alakar su da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari wajen kokarin magance Shi’anci a Nijeriya.
A cikin audio din jawabin nasa, Shaikh Gero ya bayyana cewa: “Iran komai suna iya yi, shi yasa da suka gayyaci shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, muka yi ‘meeting’ tare da shi, muka fada masa yai hattara da wadannan mutane. Muka fada mai kaji-kaji-kaji (dangane da Shi’a). Yace to zai lura. Muka ce to in kuma ka je Iran kar ka sa baqaqen kaya, don yana cikin hanyar yaudarar su, za su maka hoto su yada ma Duniya cewa ai kai mamba ne daga cikinsu.”
Gero yace: “Duk alkawuran da ya mana, da ya je Iran ya cika su, kun gan shi a setilait cikin fararen kaya.” Ya cigaba da cewa: “Da (Buhari) ya dawo ya kira wasu daga cikinmu da mukai ‘meeting’ da shi (kan ya tafi), ni ban samu zuwa ba, yace duk abin da kuka fada mana kun rage, ni na je Iran na gani da ido na, wallahi babu Musulunci.”
Mai karatu, ba za mu tambayi kanmu cewa mene ne damuwar shugaban qasar Nijeriya, qasar da ba ba ruwanta da Allah da addini, ba ruwanta da me kake bautawa a qa’idarta da kuma Aqidar Shi’anci ko Mazhabar Ahlulbait (AS)?
Kuma hatta taron da Buhari ya je Iran taro ne na wasu kasashe guda 8 masu arzikin man fetur a Duniya. Ko da yake ya gana da shugaban addini na qasar Iran, Sayyid Ali Khamene’I (H), amma sam ganawarsu bata da alaqa da Musulunci ko Shi’anci, face ya bashi shawarwari ne a kan muhimmanin dogaro da kai da nesantar kasashe masu yin mulkin mallaka irin su Amurka.
— Qarqarewa:
Daga abin da ya bayyana ga mai karatu, zai fahimci cewa tabbas waqi’ar Zariya da aka dira a kan Shaikh Zakzaky da almajiransa, wani yunquri ne na qoqarin kawar da Harka Islamiyyah da abin da suka kira Shi’anci, ko tasirin Iran a Afirka. Ya fi karfin wani wasan kwaikwayo na cewa wai an tare hanya ne kawai sai hakan ya auku kuma har yau bai kawo karshe ba!
Don haka ne ma duk abin da suka yi na kokarin ganin bayan Harkar ta Musulunci abu yaci tura, har yanzu ba su hakura ba. Suna cigaba da tsare Shaikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah, duk da cewa babbar kotun tarayya a Abuja ta ba da umurnin a sake shi, amma sun take dokar, yanzu ma sun komar da shi Kaduna ne sun gurfanar da shi a gaban wata kotu suna masa haramtacciyar shari’ar da bata da makama.
— Daga littafin Kisan Kiyashin Zariya Da Abubuwan Da Suka Biyo Baya, na Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H).
0 Comments