Haramtacciyar kasar Isra'ila ta kashe mutum 76 'yan gida daya a Gaza

 Haramtacciyar kasar Isra'ila ta kashe mutum 76 'yan gida daya a Gaza.



Wani hari ta sama da Isra’ila ta kai ya yi sanadin mutuwar mutum 76 wadanda suka fito dangi guda, kamar yadda jami’an da ke aikin ceto suka tabbatar.


Wannan na zuwa ne kwana guda bayan shugaban Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi kan cewa babu wani wuri mai aminci da mutum zai iya tsira a Gaza.


Harin wanda aka kai a gidan iyalan Mughrabi, ya yi sanadin mutuwar masu gidan 16, sai kuma mata da yara da dama.


Daga cikin wadanda suka rasu har da Issam al Mughrabi, wani babban ma’aikacin Majalisar Dinkin Duniya, inda aka kashe shi da matarsa da ‘ya’yansa biyar.

Post a Comment

0 Comments