Hare-haren ‘yan bindiga sun tilasta wa kungiyar likitoci ta MSF kwashe ma’aikatanta daga Zamfara

Hare-haren ‘yan bindiga sun tilasta wa kungiyar likitoci ta MSF kwashe ma’aikatanta daga Zamfara

Kungiyar MSF ta ce karuwar hare-hare a jihar Zamfara ta tilasta mata janye ma’aikatanta daga garin Zurmi, inda aka yi gumurzu sosai a kusa da asibitin da suke aiki.

Mai magana da yawun MSF ya ce sun kwashe ma’aikata shida da ayyukansu ba su zama dole ba yayin da wasu ma’aikatansu ‘yan kasashen waje da kuma ‘yan kasa ke ci gaba da zama a yankin.

Gumurzun da ake yi tsakanin ‘yan bindiga da sojojin Nijeriya a arewa maso yammacin kasar ya tilasta wa kungiyar likitocin duniya mai bayar da agaji ta Medecins sans Frontieres (MSF) kwashe wasu daga cikin ma’aikatanta daga jihar Zamfara, kamar yadda ta bayyana ranar Juma’a.

Matakin ya nuna irin mawuyacin halin rashin jinkai da mutanen yankunan da ‘yan bindiga ke kai hare-hare suke ciki.

‘Yan bindigar sukan kai hari a gidaje da gonaki da makarantu inda suke sace mutane domin karbar kudin fansa, a wasu lokutan kuma su kashe su.

Kungiyar MSF ta ce karuwar hare-hare a jihar Zamfara ta tilasta mata janye ma’aikatanta daga garin Zurmi, inda aka yi gumurzu sosai a kusa da asibitin da suke aiki.

"Mun kwashe wasu ma’aikatan MSF sakamakon hatsarin da suke fuskanta yayin gudanar da ayyukansu, abin da ya sa ba za su iya yin ayyukan yadda suka kamata ba," in ji sanarwar kungiyar.

Mai magana da yawun MSF ya ce sun kwashe ma’aikata shida da ayyukansu ba su zama dole ba yayin da wasu ma’aikatansu ‘yan kasashen waje da kuma ‘yan kasa ke ci gaba da zama a yankin.

Jami’an gwamnatin Zamfara da ‘yan sanda ba su yi martani game da batun ba da aka nemi karin bayani a gare su.

Sai dai gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya wallafa sako a shafinsa na sada zumunta inda yake bayyana damuwarsa game da hare-haren baya-bayanan nan a Zurmi, Maru, da Tsafe.

Post a Comment

0 Comments