Hukumar Hisbah ta karamar Hukumar sabon Gari zaria ta samu nasarar ceto wata budurwa mai suna Rabi'ah Salisu ƴar kimanin shekaru 22 da wani saurayi mai suna Joe Abdulmumin ɗan kimanin shekaru 30 ya ɓoyeta kimanin shekaru 7

 Hukumar Hisbah ta karamar Hukumar sabon Gari zaria ta samu nasarar ceto wata budurwa mai suna Rabi'ah Salisu ƴar kimanin shekaru 22 da wani saurayi mai suna Joe Abdulmumin ɗan kimanin shekaru 30 ya ɓoyeta kimanin shekaru 7 da suka wuce a gidan su dake unguwar Dogarawa a karamar Hukumar sabon Gari,kuma har ta haifa masa yara guda uku(3) biyu2 mata ɗaya 1 namiji a yau 28/12/2023 da misalin karfe 1:30pm.(na Rana).



A hirar mu da mahaifinsa wanda yake makaho ne ya shaida mana cewa yayi yayi ɗan nasa ya mayar da yarinyar amma abin yafi karfin sa.

Mahaifin ya shaida mana cewa a salinsa ɗan garin Madobi ne dake Jihar Kano Amma kuma shi ba musulmi bane Kirista ne.


Har ila yau munyi hira da ƴaƴan Rabi'ah Malam Abdullahi Salisu kuma yace mana shekaru bakwai kenan suna neman ƙanwarta su da ta baro gida daga gidan su a unguwar jaba daga nan basu ƙara jin ɗuriyar ta ba sunyi adduah daga baya suka mayar da komai zuwa ga mahaliccin su.


Tuni dai muka mika shi ga Jimi'an tsaron ƴan sanda domin cigaba da bincike da kuma gurfanar dashi gaban ƙulliya domin ya girbi sakamakon wannan mummunan aikin da ya aika ta.


Allah Ya ƙara mana Nasara ya kuma kare mu daga sharrin bin son zuciya.

Post a Comment

0 Comments