Hukumar Kwastam ta fara binciken jami’in da aka ɗauka a kyamara yana karɓar rashawa

Hukumar Kwastam ta fara binciken jami’in da aka ɗauka a kyamara yana karɓar rashawa
Hukumar Kwastam ta Najeriya, NCS, ta fara gudanar da bincike kan wani lamari da ya faru a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas, inda aka ga wani jami’i yana neman cin hancin Naira dubu 5,000 daga wani fasinja.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, babban Sufeton Kwastam, Abdullahi Maiwada, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Talata a Legas.

A cewar, Maiwada, wannan dabi’a ta tada hankalin jama’a, kuma sun himmatu wajen tabbatar da cikakken bayani.

“Bincike na farko ya nuna cewa lamarin ya faru ne a ‘New Terminal’ a cikin dakin tsumayen tashin jirgin na filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas, kuma fasinjan da abin ya shafa ya dauki hoton bidiyon.

“bidiyon ta nuna yadda jami’in ya zubar da mutuncint kakinsa, inda ya ke neman Naira 5,000 ga wani fasinja domin ya yi masa aiki cikin gaggawa.

“Muna so mu tabbatar da cewa jami’in da ake zargi ma’aikacin Hukumar Kwastam ta Najeriya ne, wanda aka kai shi ya yi aiki a filin jirgin sama na Murtala Mohammed,” in ji shi.

Post a Comment

0 Comments