Isra'ila ta ce an kashe karin sojojinta takwas a arewacin Gaza.

 Isra'ila ta ce an kashe karin sojojinta takwas a arewacin Gaza.

An kashe karin sojojin Isra’ila takwas a Gaza, daga ciki har da mai mukamin Laftanar Kanal da kuma wani Manjo.



Isra'ila ta ce an kashe karin sojojinta takwas a arewacin Gaza


Rundunar sojin Isra’ila a ranar Laraba ta sanar da cewa an kashe karin sojojinta takwas, ciki har da kwamandoji a arewacin Gaza a sa’o’i 24 da suka gabata.


Rundunar sojin ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar.


Kafar watsa labarai ta Isra’ila KAN ta sanar da cewa daga cikin sojojin na Isra’ila da aka kashe har da Laftanar Kanal Tomer Grinberg mai shekara 35 da Manjo Moshe Avram da Roei Meldasi mai shekara 23 wadanda duka kwamandoji ne.

Post a Comment

0 Comments