Isra'ila ta kashe mutane da dama bayan wa'adin yarjejeniyarta da Hamas ya kare

 KAI-TSAYE: Isra'ila ta kashe mutane da dama bayan wa'adin yarjejeniyarta da Hamas ya kare.



Falasdinawa akalla shida ne suka mutu yayin harin da Isra'ila ta kai ta sama a birnin Rafah da ke kudancin Gaza, kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar lafiya ta Falasdinu Ashraf al Qudra ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.


A gefe guda, an kashe kananan yara biyu a hari ta sama da Isra'ila ta kai a Birnin Gaza, a cewar Fadel Naim, wani likita a asbitin Al Ahli, a yayin da aka ci gaba da gumurzu tsakanin Hamas da Isra'ila bayan karewar wa'adin tsagaita wuta.


Dakarun Isra'ila sun kai jerin hare-hare a gidajen kwanan jama'a a Gaza, abin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.


Wasu majiyoyi sun ce an garzaya da gawawwaki hudu da kuma wasu mutane asibitin Abu Youssef Al Najjar da ke birnin Rafah bayan dakarun Isra'ila sun kai musu hari.

Isra'ila da Hamas sun ci gaba da gumurzu a Gaza



Rundunar Sojojin Isra'ila ta tabbatar da cewa ta ci gaba da kai hare-hare a arewacin Gaza da jiragen yaki da tankoki da kuma jiragen ruwan soji

Ta bayyana haka ne ranar Juma'a bayan wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da Hamas ya kare.

Bayanai sun ce yaki ya kaure tsakanin sojojin Isra'la da Falasdinawa masu fafutuka a arewaci da tsakiyar Gaza bayan wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta ya kare

Post a Comment

0 Comments