Isra'ila ta kashe tare da jikkata Falasdinawa 750 a Gaza cikin sa'o'i 24

 Isra'ila ta kashe tare da jikkata Falasdinawa 750 a Gaza cikin sa'o'i 24

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 81 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 20,674, galibinsu mata da kananan yara, sannan sun jikkata fiye da mutum 54,536.


Isra'ila ta kashe tare da jikkata Falasdinawa 750 a Gaza cikin sa'o'i 24


Akalla Falasdinawa 250 aka kashe tare da jikkata wasu 500 sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai a zirin Gaza cikin sa'o'i 24 da suka gabata, in ji ma'aikatar lafiya ta Gaza.


A cikin wata sanarwa da kakakin ma'aikatar Ashraf al-Qudra ya fitar, ya ce kungiyoyin likitocin ba su iya kula da dukkan wadanda suka jikkata da suka isa asibitoci ba, yayin da ya ce suna fama da kula da nau'ikan raunukan da ba su gani ba a yaƙin da suka gabata.


Ya ƙara da cewa adadin gadajen kwantar da marasa lafiya a asibitocin da ke aiki a kudancin Zirin Gaza ya kai kashi 350 cikin 100. Al-Qudra ya kuma yi nuni da cewa, agajin jinƙai da na jinya da ke isa Gaza ba ya biyan buƙatun asibitocin ba.


Da sanyin safiyar Talata, mazauna Falasdinu sun ba da rahoton wasu hare-hare ta sama a kusa da asibitin Nasser da ke Khan Younis, cibiyar kiwon lafiya mafi girma a kudancin Gaza.


Jami'an kiwon lafiya na Falasdinu sun ce mutane bakwai ne suka mutu a wani harin sama da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai a wani gida da ke unguwar Al-Amal a Khan Younis.

Post a Comment

0 Comments